Yana rike da wani tsuntsu a hannunsa mai suna Koel na yankin Asia, jami’in kula da dabbobin jeji Zaheer Ahmed ya miƙar da fukafukan tsuntsun a matsayin wani binciken lafiya don farfaɗo da tsuntsayen da suka kamu da rashin ruwa ko tsananin zafi a babban birnin Pakistan.
Pakistan — ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi fuskantar illolin sauyin yanayi — inda ta fuskanci shekarar da ta kasance ta biyu mafi zafi tun 1960 a shekarar 2025, a cewar bayanan gwamnati.
Yanayin zafi a Islamabad a wannan bazara ya ketare maki 40 a ma’aunin Celcius.
"A da, saboda tayar da jirgin leda, zaren yana lalata fukafukan su," in ji Sakhawat Ali, daraktan Hukumar Kula da Namun Daji ta Islamabad, wadda ke kula da wurin ceto da dabbobin daji na Margallah a Islamabad.
"Amma a cikin shekara ɗaya ko biyu da suka gabata, mafi yawan matsalolin da muka fi karɓa sun shafi tsuntsaye da suka yi jinya saboda rashin ruwa sakamakon zafi."
Cibiyar ceto dabbobin jeji, wadda ke ƙasan tsaunin Margalla, a da wurin ne gidan namun daji na Islamabad da aka sani da halin muni inda aka bar giwaye da zakuna marasa ciyarwa cikin kurkuku.
An rufe gidan namun daji a 2020.
A kan filin da ciyayi suka mamaye inda har yanzu akwai dinosaur da aka sassaƙa, an kawo dabbobi daga ko’ina cikin Pakistan don a farfado da su, ciki har da dabbar bear da birai waɗanda masu su suka zalunta.
Masana kimiyya na gargadin cewa akwai jerin yanayi da ake shiga masu tsanani irin tsananin zafi na ƙara yawaita da tsananta sakamakon sauyin yanayi da bil’adama suka jawo.
Ahmed ya ce cibiyar na iya karɓar kiran waya har sau 30 a rana a lokacin rani daga mazauna kan dabbobin da ke cikin matsala, ciki har da tsuntsaye, sannan ya ce manyan manufofinsu sun haɗa da ba da kulawar likita, abinci da ruwa.
Ana ajiye waɗannan tsuntsaye a keɓe, wani lokaci har na ɗan makonni, har sai an ga sun samu ƙarfi su isa a sake su.
Tsuntsaye na fuskantar karin haɗari daga gobarar daji, wanda zai iya haɗuwa da lokutan barbararsu, in ji Ahmed.
"Har ma sheƙar tsuntsaye da yawa sun ƙone. Tsuntsayen kansu ma sukan ƙone daga wuta," in ji Ahmed. "Don haka ana lalata duk muhalli ɗinsu."
Ali ya ƙarfafa mazauna yankin da su riƙa ajiye kwanonin ruwa a waje domin tsuntsayen da ke rayuwa tare da mutane su sha ruwa, su yi wanka, kuma su samu sanyi.
Hukumar Kula da Namun Daji ta Islamabad, wata hukuma ta gwamnati, na gudanar da bincike kan ko sauyin yanayi na kawo cikas ga lokutan barbara da kuma hanyoyin samun abinci na tsuntsaye, lamarin da ka iya rage yawan adadinsu.



















