| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Kwamitin tattaunawa na Libiya ya cim ma matsaya kan tsarin ɗaukar shugaban hukumar zaɓe
Kwamitin na son amfani da wani tsarin zaɓe da zai samu karɓuwa ta fannin fasaha da siyasa yayin zaɓukan shugaban ƙasa da na 'yanmajalisa.
Kwamitin tattaunawa na Libiya ya cim ma matsaya kan tsarin ɗaukar shugaban hukumar zaɓe
Yarjejeniyar ta baya bayan nan wani ɓangare ne na ƙoƙarin da MƊD ke jagoranta na samar da wani yanayin zaɓe don kawo ƙarshen rarrabuwar siyasa Libya.

Mambobin Kwamitin Tattaunawa na 4+4 na Libiya sun amince ranar Laraba kan wani tsarin ɗaukar sabon Shugaban Babbar Hukumar Zaɓe ta Ƙasar (HNEC) bayan ƙoƙarin aiwatar da tsarin da aka amince da shi a baya ya ci tura.

An cim ma matsayar ne a lokacin zama na bakwai na kwamitin a babban birnin Tunisiya, Tunis, in ji wata sanarwar da ofishin MDD a Libya (UNSMIL) ya fitar.

Kwamitin ya shafe watanni yana tattaunawa bayan wakiliyar MDD ta musamman Hanna Tetteh ta shaida wa Ƙwamitin Tsaro na MDD ranar 22 ga watan Afrilu cewa ta tattauna da kaɗan daga cikin masu ruwa da tsaki na Libya kan su bayyana hanyoyin aiwatar da matakai biyu na shirin MDD.

Shirin, wanda aka bayyana a ranar 21 ga watan Agustan shekarar 2025, an gina shi ne kan ginshiƙai uku: amincewa da wani tsarin zaɓe da zai samu karɓuwa ta fannin fasaha da siyasa yayin zaɓukan shugabana ƙasa da na 'yanmajalisa, da haɗa kan cibiyoyin ƙasa ta hanyar kafa gwamnatin haɗin gwiwa, da kuma ƙaddamar da tattaunawa ta ƙasa.

Daftarin yarjejeniyoyi

UNSMIL ta ce mahalarta zaman na ranar Laraba, wanda Tetteh ta jagoranta, sun cim ma matsaya kan tsarin naɗin shugaban hukumar zaɓe ta ƙasar.

“Sun kuma ci gaba da tuntuɓar juna bisa sauran tanade-tanaden daftarin yarjejeniyar na ƙarshe, inda dukkan ɓangarorin suka yarda su ci gaba da tattaunawa a mako mai zuwa a Tunis,” in ji sanarwar.

A lokacin zamansu na farko a birnin Rome ranar 29 ga watan Afrilu, mambobin kwamitin 4+4 sun yarda su sake fasalin hukumar zaɓen ƙasar da kuma ba da shawarar cewa Antoni Janar na ƙasar Al-Siddiq Al-Sour ya ba da sunan wani sabon shugaban hukumar daga cikin manyan alƙalai da suka yi fice da ƙwarewa da kuma rashin nuna bambanci.

Sai dai kuma, daga baya a yayin zamansa na shida a Tunis ranar 14 ga watan Yuli, kwamitin ya sanar da cewa an dakatar da ƙaddamar da waccan yarjejeniyar.

Yarjejeniyar ta baya bayan nan wani ɓangare ne na ƙoƙarin da MDD ke jagoranta na samar da wani yanayi na zaɓuka da zummar kawo ƙarshen rarrabuwar kan Libiya a siyasance.

Rumbun Labarai
Me samar da lantarki ke nufi ga Afirka?
Chivayo: Rayuwar attajirin da ya mutu, wanda ya taba ba wa wani mawaki $1m don yin wasa a biki
Hare-haren 'yanta'adda sun kashe gomman sojoji a wurare biyu a Nijar
An zaɓi matasan Nijar 500 domin samun horo a kyauta don koyon sana’o’i a Aljeriya
Fiye da mutum 55,000 daga Sudan sun tsere zuwa gabashin Chadi don gudun hijira
Wasu karin mayakan RSF sun sauya sheka zuwa Rundunar Sojin Sudan bayan sun gamu da 'masifu'
Ana samun ƙaruwar Ƙasashen Yamma masu goyon bayan biyan diyyar cinkin bayi: Ghana
Shugaban Sudan ta Kudu Kiir ya rusa gwamnatin haɗin kan ƙasar
Zakuna goma sun mutu a wani gandun dabbobi da ke Tanzania
Sojojin Sudan sun harbo jirgi maras matuƙi da lalata motocin yaƙin RSF
An kama mutum 10 ciki har da jami’an kwastam 4 kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi a Ghana
Rundunar Operation Damissa a Nijar ta lalata maɓoyar mayaƙan ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai a Dosso
Shugaban Nijar Tiani ya sauya wasu ministocinsa
Shugabar Majalisar Dokokin Cabo Verde ta zama shugabar ƙasar ta riƙo
Harin ta'addanci ya yi ajalin sojojin Mali aƙalla 50, da sojojin haya na Rasha biyar
Ƙasashen Afirka biyar sun kawar da yaɗuwar cutar shan inna, amma ba a gama yaƙin ba
Nabil Neghiz ya zama kocin tawagar Mena ta Nijar
Fiye da mutum 7,000 sun kamu da annobar Ebola a Jamhuriyar Kongo
Shugaban Nijar ya naɗa Birgediya Janar Mamane Sani Kiaou a matsayin sabon shugaban hafsan sojoji
FIFA ta musanta iƙirarin Maroko na 'karɓar baƙuncin' wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya na 2030