Mai son rayuwar alfarma da ƙawa, mai burin cim ma manyan nasarori kuma mai kusanci da manyan mutane, attajirin Zimbabwe Wicknell Chivayo ya rasu.
Chivayo ya mutu tare da matarsa, Lucy Muteke, da wasu mutane da dama a wani hatsarin jirgin helikwafta a Marondera, gabashin Harare, ranar Laraba, 30 ga Satumba.
Ya kasance ɗaya daga cikin fitattun attajiran sabon ƙarni na ’yan kasuwar Zimbabwe masu yawan nuna arzikinsu. Sau da dama Chivayo kan bayyana kansa a matsayin “centi-millionaire”, wato mutum da dukiyarsa ta kai daruruwan miliyoyin daloli, yana kuma da burin zama attajiri mamallakin biliyoyin daloli.
An san attajirin da salon rayuwarsa mai tsada da kuma fariya da nuna arzikinsa, inda yake bayar da kyaututtukan motoci na alfarma da makudan kuɗaɗe, lamarin da ya zama wani ɓangare na shahararsa a idon jama'a.
Chivayo ya kuma kasance cikin da'irar manyan mutane, inda ya yi mu'amala da shugabannin ƙasashen Afirka, ciki har da Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, Shugaban Kenya William Ruto, Shugabar Tanzania Samia Suluhu Hassan da kuma Shugaban Najeriya Bola Tinubu.
A wani misali na kusancinsa da Ruto, an ga shugaban Kenya a wani bidiyo da ya yadu sosai yana tuƙa motar da Chivayo ke ciki a lokacin da ya ziyarci Kenya domin halartar bikin neman auren ’yar Ruto, Charlene.
Bayan mutuwar Chivayo, Ruto ya yi alhini, inda ya ce ya ji matuƙar baƙin ciki da rasuwar “aboki na ƙwarai wanda ɗuminsa ya taɓa rayuwar mutane da dama.”
Chivayo ya yi fice a fannonin gine-ginen ababen more rayuwa da makamashi, inda ya samu manyan kwangilolin gwamnati a wasu ƙasashe. Shi ne ya kafa kamfanin Intratrek Zimbabwe Ltd, wanda ya fi mayar da hankali kan aikin injiniya da makamashi mai sabuntawa.
Sai dai rayuwarsa ta kasance cikin cece-kuce. Ya taɓa shafe shekaru uku a gidan yari kusan shekaru 20 da suka gabata bayan an same shi da laifin karkatar da kuɗaɗe ta haramtacciyar hanya.
An kuma sha ambaton sunan Chivayo dangane da wasu kwangilolin da aka yi ta cece-kuce a kansu a Kenya da Zimbabwe a baya-bayan nan, ko da yake ba a tuhume shi da wani laifi a kan waɗannan batutuwa ba.
Mutuwarsa a hatsarin ta girgiza mutane da dama a kudanci da gabashin Afirka.
Gidan rediyon gwamnatin Zimbabwe, ZBC, ya ambato mai magana da yawun iyalan Chivayo, Herbert Chivayo, yana cewa mutane biyar ne ke cikin jirgin, ciki har da mataimakin attajirin da matukan jirgi biyu.
Sai dai kakakin gwamnatin Zimbabwe, Nick Mangwana, ya ce tun da farko mutane shida ne ke cikin jirgin mai zaman kansa.
Mahukunta sun ce babu wanda ya tsira daga hatsarin, kuma har yanzu ba a gano musabbabin hatsarin ba. Rundunar ’yan sandan Zimbabwe ta ce za a gudanar da bincike domin gano abin da ya haddasa hatsarin.
Chivayo da matarsa suna kan hanyarsu ne daga gidansu da ke yankin karkara na Gandami zuwa Harare, mai tazarar kusan kilomita 144, inda suke gina wani katafaren gida gabanin bikin cikar attajirin shekaru 44 a watan Nuwamba.
Shahararren mawaƙin Zimbabwe Thomas Mapfumo ma ya isa ƙasar daga Amurka a wannan makon domin halartar wasu shagulgulan bikin ranar haihuwar Chivayo da aka shirya kashe dala miliyan ɗaya a kansu.
Wannan ne zai kasance karo na farko da mawakin mai shekaru 81 zai ziyarci Zimbabwe cikin sama da shekaru goma.
Sai dai yanzu waɗannan shirye-shirye sun rushe, yayin da alhini da ta'aziyya ke ci gaba da zuwa bayan rasuwar attajirin.






















