Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Trabzonspor da ke Turkiyya ta tabbatar a ranar Alhamis cewa ta ɗauki Tauraron ƙwallon ƙafa na Masar Mohemed Salah kan wata yarjejeniya da a ƙarƙashinta zai riƙa ɗaukar dala miliyan 19.6 (€17 miliyan) a duk kakar wasanni.
Ɗanwasan na Masar, Salah ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru biyu ne bayan ya bar Liverpool ta Ingila a ƙarshen kakar bara.
Salah zai samu dala miliyan $19.6 duk kakar wasanni, wato albashin dala miliyan $11.5, da bonos ɗin dala miliyan $8. Haka nan, yana da damar samun garaɓasar gwargwadon ƙoƙarinsa, tare da kashi 20 daga amfani da sunansa.
Bayan kwashe shekaru tara a gasar Firimiya, mashahurin ɗanwasan mai shekaru 34 ya iso Turkiyya don buga babbar gasar ƙasar ta Super Lig, a matsayinsa na ɗanwasan da ba shi ƙungiya.
Tun a ranar Laraba ne Salah ya isa birnin Trabzon da ke bakin teku, kafin ya sanya hannu ranar Alhamis a sauyin sheƙar da ya ja hankalin masoya ƙwallo a duniya.
Salah ɗanwasan gaba ne mai farin jini, kuma ya samu nasarori da dama a ƙwallo, cikin har da lashe gasar Firimiya sau biyu, da gasar Zakarun Turai guda, da FA ɗaya, da Carabao ɗaya.
Batun tagomashi
Ɗanwasan ya samu gagarumar tarba daga dubban masoya Trabzonspor bayan saukar sa a filin jirgi sanye da rigar ƙungiyar, abin da ya ƙayatar da shi matuƙa.
Da yake jawabi yayin bikin tarbar tasa, Salah ya zayyana burukansa, yana cewa, "Ina matuƙar murna da kasancewata a wannan ƙayataccen waje. Ba na iya tuna na ga irin wannan taron kafin yau."
Gabanin barin Liverpool, Salah ya ci ƙwallaye 257 da tallafin ƙwallo 123 a wasanni 442 a duka gasannin da ya buga.
Sai dai a kakar ƙarshe da ya buga a Anfield tagomashinsa ya yi ƙasa, inda ƙwallo bakwai kacal ya ci a wasanni 27, wanda shi ne karo na farko da ya ci ƙwallaye ƙasa da 10 a kaka guda a Liverpool.
Sai dai Mohamed Salah ya ci gaba da kasancewa haziƙi abin alfahari a fagen ƙwallo, kasancewarsa kyaftin ɗin tawagar Masar a gasar Kofin Duniya ta 2026 da aka fitar da su a zagayen ‘yan-16.
Trabzonspor ce ta lashe kofin Turkish Cup a kakar da aka kammala, inda t ƙare lig da maki takwas a ƙasan Galatasaray da ta lashe kofin.
Rabon da Trabzonspor ta lashe gasar Super Lig tun kakar 2021-22. Don haka a bana suna fatan zuwan Salah ya ƙara musu armashi da tagomashi, inda za su nemi kofuna a gasanni ciki har da gasar Europa.















