Ƙwallon da aka yi amfani da ita wajen jefa kwallon da Argentina ta zura a ragar Ingila ta shafe shekaru da dama a hannun alkalin wasan da ya gaza ganin magudin da aka yi da hannu.
Ƙwallon da aka yi amfani da ita wajen zura kwallo a ragar Ingila wanda ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Argentina, marigayi Diego Maradona, ya yi da hannu a Gasar Kofin Duniya na FIFA ta shekarar 1986, an sayar da ita a kan dala miliyan 3 da dubu 350, a cewar Heritage Auctions.
An yi amfani da ƙwallon mai suna Adidas Azteca ne a lokacin da Argentina ta doke Ingila da ci 2-1 a wasan kusa da na ƙarshe, inda Maradona ya jefa ƙwallaye biyu da tarihi ba zai manta da su ba a Gasar Kofin Duniya.
Wurin da aka yi gwanjon kwallon mai suna Dallas House ya sayar da ƙwallon, wadda ƙwararru suka tabbatar da kamanninta da hotunan da aka ɗauka a lokacin wasan, kan dala miliyan uku da dubu 350 a ranar Asabar.
Farashin da aka sayar da kwallon ya yi ƙasa sosai da ƙiyasin farko kafin gwanjon wanda aka yi hasashen zai kai a ƙalla dala miliyan 10.
Kafin gwanjon, Heritage Auctions ya bayyana ita wannan ƙwallon a matsayin wadda ta fi kowace ƙwallo shahara a kowane irin wasan motsa jiki, sannan ya ƙara da cewa tana iya zama kayan ƙwallon ƙafa mafi tsada da aka taba sayarwa.
Ƙwallon farko da Maradona ya jefa a kan Ingila ta zama sananniya bayan da ya yi amfani da hannunsa na hagu wajen tura ƙwallon har ta wuce mai tsaron gida Peter Shilton, inda alƙalai suka amince da ƙwallon.
Bayan mintuna huɗu, kyaftin ɗin na Argentina ya karɓi ƙwallon daga ɓangarensa na fili sannan ya gudu da ita ta gaban ƴanwasan Ingila guda biyar kafin ya jefa ƙwallon da daga baya aka zaɓa a matsayin “Ƙwallon Mafi Shahara a Ƙarni” ta Gasar Kofin Duniya na FIFA.
Wannan ƙwallon ta shafe shekaru 36 a hannun alkalin wasa ɗan kasar Tunisiya, Ali Bin Nasser, wanda ya jagoranci wasan. A baya an taɓa sayar da ita kan fam miliyan biyu (dala miliyan 2.37) a a London a shekarar 2022.
Rigar da Maradona ya sanya a wannan wasan ita ma an sayar da ita kan kusan $9.3 million a Sotheby’s daga baya a shekarar 2022.
WASANNI
2 minti karatu
An sayar da ƙwallon da Maradona ya ci Ingila da hannu a kan $3.35M
An yi amfani da ƙwallon mai suna Adidas Azteca ne a lokacin da Argentina ta doke Ingila da ci 2-1 a wasan kusa da na ƙarshe, inda Maradona ya jefa ƙwallaye biyu da tarihi ba zai manta da su ba a Gasar Kofin Duniya.

Rumbun Labarai















