| Hausa
WASANNI
3 minti karatu
Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafar Nijeriya Musa Gusau ya yi murabus
Shugaban Hukumar Ƙwallon Kafa ta Nijeriya Musa Gusau da Babban Sakataren Hukumar Mohammed Sanusi da sauran 'yan kwamitin zartarwarsa sun yi murabus yayin da zarge-zargen cin hanci suka dabaibaye hukumar.
Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafar Nijeriya Musa Gusau ya yi murabus
Matakin Ibrahim Musa Gusau na zuwa ne wata guda kafin hukumar ta gudanar da babban zaɓenta na gaba.

waShugaban Hukumar Kwallon Kafar Nijeriya (NFF) ya yi murabus a ranar Alhamis, a daidai lokacin da yake fuskantar zarge-zargen cin hanci da kuma samun sakamako maras gamsarwa da ƙungiyoyin ƙwallon kafar ƙasar suka samu, ciki har da Super Falcons a baya-bayan nan.

Matakin Ibrahim Musa Gusau na zuwa ne wata guda kafin hukumar ta gudanar da babban zaɓenta na gaba.

Kafofin yaɗa labarai na cikin gida sun ruwaito cewa wasu mambobin kwamitin gudanarwar NFF ma sun yi murabus daga muƙamansu.

Gusau ya shaida wa manema labarai a Abuja cewa, “Na yanke shawarar yin murabus daga matsayina na shugaban NFF,” inda ya ƙara da cewa ya “shawarci” sauran mambobin kwamitin da su ma su yi murabus.

Kafofin yaɗa labarai na cikin gida sun ruwaito cewa Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) na gudanar da bincike kan NFF kan zargin karkatar da Naira biliyan 17, kimanin dala miliyan 12.7, da hukumar ta karɓa daga gwamnati a shekarar 2024 domin biyan bashin kuɗaɗen da ake bin hukumar ga ‘yan wasan ƙasa da jami’anta.

Duk da cewa Nijeriya na daga cikin manyan ƙasashen da ke kan gaba a ƙwallon kafa a Afirka, hukumar ta NFF ta daɗe tana fuskantar zarge-zargen cin hanci da rashin gudanar da harkoki yadda ya kamata.

‘Yanwasan ƙasa da masu horaswa sun sha gudanar da zanga-zanga a bainar jama’a saboda rashin biyan su alawus-alawus.

Sabon rikicin ya biyo bayan gazawar Super Falcons wajen samun tikitin shiga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata ta 2027.

Tawagar Nijeriya, wadda ita ce zakarar Afirka mai rike da kambu kuma ta lashe Kofin Afirka na Mata sau 10, ta fice daga gasar a matakin daf da na kusa da na ƙarshe, kafin daga bisani ta sha kashi da ci 2-1 a hannun Afirka ta Kudu a wasan neman tikitin shiga gasar.

Wannan rashin nasarar na nufin Nijeriya za ta rasa shiga gasar ta duniya a karon farko tun bayan fara gasar a shekarar 1991.

Har ila yau, tawagar maza ta ƙasa, Super Eagles, ba ta samu damar shiga Gasar Cin Kofin Duniya ba tun bayan bayyanarta ta ƙarshe a shekarar 2018, inda ta kasa samun tikitin shiga gasar 2022 da ta 2026.

Duk da yin murabus, Gusau ya kare yadda ya jagoranci hukumar, inda ya ɗora alhakin matsalolin kuɗin hukumar kan tsadar rayuwa da ƙalubalen tattalin arzikin ƙasar, da kuma sauye-sauyen farashin musayar kuɗaɗen waje.

Ya kuma sanar da wata yarjejeniya ta haɗin gwiwa da Adidas, wadda za ta riƙa bai wa Nijeriya dala miliyan 4.5 a kowace shekara.