Danwasan Portuagal da ke wasa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Al Nassr, Cristiano Roanldo, ya fara kakarsa ta 25 a fagen ƙwallon ƙafa da zura ƙwallonsa na 977 a tarihin wansansa.
Cristiano ya taso daga benci ne inda ya taimaka wa Al Nassr lallasa AlRiyadh da 4-0 a fafatawar lig ɗin Saudiyya da suka yi ranar Jumma’a.
Ɗanwasan mai shekara 41 da haihuwa ya shiga wasan ne minti 62 da fara wasa yayin da kulob ɗinsa ke gaba da ƙwallaye 3 da Abulelah Al-Amri da Angelo Gabriel da Joao Felix suka zura a raga.
Saura minti bakwai kafin a ƙarƙare wasan ne lokacin Ronaldo ya kwantar da wani kurosin daga Aiman Yahya kafin ya zura ƙwallon a raga cikin ƙwarewa daga yadi na takwas.
A halin yanzu Ronaldo ya shafe kaka 25 na ƙwallon ƙafa yana zura ƙwallo a raga.


















