Manceshter United ta fara kakar gasar Firimiya ta bana da shan kaye a hannun Hull City wadda ta doke Red Devils da ci biyu da nema a karawar da suka yi ranar Asabar.
Ɗan wasan Nijeriya, Semi Ajayi ne ya fara zura ƙwallo a ragar Manchester United minti 17 da fara wasa, lamarin da ya sa Hull City wadda a bana ta dawo gasar Firimiya tun shekarar 2017 ta yi gaba da Manchester United.
Duk da cewa Hull City ta rasa ‘yan wasa 10 sakamakon jinya, ba ta bai wa United damar ramawa ba har sai da ta ƙara mata ƙwallo ɗaya a lokacin da Nobel Mendy ya tura ƙwallo ragar United da kansa minti 38 da fara wasa.
An tafi hutun rabin lokaci Hull City na da ƙwallaye biyu yayin Manchester United ba ta ci ko ɗaya ba.
Bayan an dawo daga hutun rabin lokacin, United ta sako Marcus Rashford wanda ya dawo daga buga wasan aro a Barcelona, amma shigarsa wasan ta kasa taimaka wajen farke ko ƙwallon ɗaya daga cikin biyun da Hull ta ci United.
Duk da cewa Manchester United ta rike kashi 72 cikin 100 na ƙwallon da aka buga, kuma ta samar da damarmaki 21, ta gaza zura ko ƙwallo ɗaya ragar Hull City, lamarin da ya sa ta sha kayen wulaƙanci a hannun ƙungiyar da ta dawo gasar Firimiya a bana.
















