Muhimman batutuwa game da ritayar Messi daga tawagar Argentina
WASANNI
3 minti karatu
Muhimman batutuwa game da ritayar Messi daga tawagar ArgentinaLionel Messi zai ci gaba da taka leda a matakin kulob tare da ƙungiyar Inter Miami ta Amurka, inda yake da kwantiragi har zuwa ƙarshen kakar shekarar 2028.
Lionel Messi ne ɗanwasan Argentina da ya fi bugawa tawagar ƙasar wasa.

Ranar Litinin shahararren ɗanwasan ƙwallon ƙafa kuma kyaftin ɗin ƙasar Argentina, Lionel Messi ya sanar da yin ritaya daga buga wa ƙasarsa wasa, inda ya bayyana cewa hakan ya masa ciwo amma dai lokaci ne ya cim masa.

Ɗanwasan mai shekaru 39, wanda ya jagoranci Argentina zuwa nasarar lashe Kofin Duniya na FIFA 2022 a Qatar, shi ne ɗanwasan tawagar Argentina da ya fi kowa bugawa ƙasarsa wasa.

Daga Agustan 2005 zuwa Agustan 2026 ya buga wasanni 207, ya ci ƙwallo 125 da tallafin ƙwallo 65, wanda ya sa ya zama ɗanwasan da ya fi kowa ciyo wa Argentina ƙwallo a tarihi.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Instagram, Messi ya ce, "Ina mai rantsuwa cewa na sadaukar da komai, ba kawai a ‘yan shekarun baya ba lokacin da muka lashe komai, amma har kafin nan ma.

“Na ba da komai da nake iyawa. Ba ni da wani ƙarin abin bayarwa, kuma akwai wasu haziƙan matasan ‘yanwasa da suka taso waɗanda ke buƙatar dama”.

Duk da cewa zai yi ritaya yana cike da alfaharin lashe kofin duniya wa kasarsa, Messi ya yi jimami inda ya ce, “Ina son tawagar ƙasata kuma zan ci gaba da ƙaunar wannan tawaga wadda na kasance wani ɓangare nata”.

Tarihin bajinta

Idan za a tuna a farkon watan jiya, Messi ya ce yana tunanin makomarsa a harkar ƙwallon ƙafa bayan mutuwar mahaifinsa, Jorge Messi, wanda ya rasu ranar 8 ga Agustan 2026 yana da shekaru 68.

Messi, wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or har sau takwas ya ce ya rubuta saƙon ritayarsa ne tun a ranar 21 ga watan Yuli, kwanaki biyu kacal bayan Argentina ta yi rashin nasara a hannun Sifaniya a wasan ƙarshe na gasar Kofin Duniya na FIFA 2026.

A tarihin wasansa, Messi ya lashe kofin Copa America guda biyu tare da Argentina.

Shi ne na biyu a jerin waɗanda suka fi zura ƙwallaye a tarihin Kofin Duniya da ƙwallaye 21, a bayan Kylian Mbappe na ƙasar Faransa mai ƙwallaye 22.

Kuma shi ne na biyu a ɓangaren ci wa ƙasa ƙwallaye a dukkan wasannin ƙasa-da-ƙasa, inda ya ci ƙwallaye 125, kuma yake bayan Cristiano Ronaldo na ƙasar Portugal wanda ya ci ƙwallaye 146.

Sai dai kuma Lionel Messi zai ci gaba da taka leda a matakin kulob tare da ƙungiyar Inter Miami ta Amurka, inda yake da kwantiragi har zuwa ƙarshen kakar 2028.

Ga masoya Messi, ga abin da ya kammala saƙon nasa, "Ina bankwana cike da kwanciyar hankali da alfahari, kasancewar ni da abokan wasana mun yi matuƙar ƙayatar da ku... Ina son ku duka. Na gode wa Allah da ya yi ni ɗan Argentina".