Hukumar Shirya Jarrabawa ta Afirka ta Yamma, WAEC ta riƙe sakamakon masu jarrabawa 167,486, wanda ke wakiltar kashi 8.59 cikin ɗari na waɗanda suka zauna jarrabawar kammala babbar sakandare ta Yammacin Afirka ta 2026, wadda aka yi da kwamfuta.
Riƙewar na zuwa ne bisa zargin maguɗin jarrabawa.
Sai dai adadin ya nuna raguwa daga kashi 9.7 cikin ɗari da aka gani a 2025.
Ranar Laraba ne shugaban ofishin ƙasa na WAEC a Nijeriya, Dr Amos Dangut ya bayyana hakan lokacin jawabinsa yayin sakin sakamakon jarrabawa a Lagos.
Dr Dangut ya ce hukumar ta riƙe sakamakon waɗanda abin ya shafa ne saboda mabambantan dalilai, ciki har da ƙaruwar amfani da wayar hannu a ɗakunan jarrabawa duk da haramcin da ke akwai sannan da shirya maguɗi a tare, a wasu makarantu.

Ya ƙara da cewa an kama wasu masu sa ido da masu kula da jarrabawa da aka samu suna taimaka wa ɗalibai wajen yin maguɗin jarrabawa, kuma za su fuskanci hukunci ta hannun ma'aikatun ilimi na jihohin da abin ya shafa.
Jimillar ɗalibai 1,959,668 daga makarantu 24,207 ne suka yi rajistar jarabawar a Nijeriya, Jamhuriyar Benin, Côte d’Ivoire da Equatorial Guinea, yayin da ɗalibai 1,950,726 suka zauna domin rubuta jarabawar.
Daga cikinsu, ɗalibai 1,200,514 (kashi 61.54 cikin 100) sun samu maki na Credit ko sama da haka a aƙalla darussa biyar, ciki har da Ingilishi da Lissafi.
Haka kuma, ɗalibai 1,687,378 (kashi 86.50 cikin 100) sun samu Credit ko sama da haka a aƙalla darussa biyar, ko da kuwa sun haɗa da Ingilishi da Lissafi ko kuma ba su haɗa da su ba.


















