| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Dakarun Nijeriya sun kama mutanen da ake zargi da kai wa 'yan Boko Haram ƙwayoyi a Borno da Yobe
Wasu daga cikin abubuwan da aka gano sun haɗa da tabar wiwi da wayoyin hannu masu yawa da na’urar cajin waya da wukake da tocila da kwalayen sigari da kapsul na Pregabalin, maganin tari da katunan shaida da katunan banki da kuɗaɗe.
Dakarun Nijeriya sun kama mutanen da ake zargi da kai wa  'yan Boko Haram ƙwayoyi a Borno da Yobe
Dakarun Nijeriya sun kama wasu mutane da ake zargi da samar wa mayakan Boko Haram da ISWAP kayyakin amfani

Rundunar Sojin Nijeriya ta ce dakarunta sun kama wasu mutane huɗu da ake zargi da kai wa mayaƙan Boko Haram da ISWAP ƙwayoyi da sauran kayayyaki a jihohin Borno da Yobe.

A sanarwa da rundunar Operation Haɗin Kai ta fitar ranar Talata, ta ce dakarunta daga bataliya ta 159 sun kama wasu mutane biyu da ake zargi kai wa ‘yan Boko Haram kayayyaki a yayi wani sintiri da bincike a Ƙaramar Hukumar Geidam ta jihar Yobe a ranar Litinin.  

Binciken farko ya nuna cewa ana zargin mutanen biyu ne da samar da miyagun ƙwayoyi da sauran kayayyaki ga mayaƙan na Boko Haram.

Wasu daga cikin abubuwan da aka gano sun haɗa da tabar wiwi da wayoyin hannu masu yawa da na’urar cajin waya da wuƙaƙe da tocila da kwalayen sigari da kapsol na Pregabalin da maganin tari da katunan shaida da katunan banki da kuɗaɗe.

A wani aiki na daban a Ƙaramar Hukumar Monguno ta Jihar Borno, dakarun sashe na 3 da bataliyar Bincike ta 242 sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da samar da kayayyaki ga mayaƙan ISWAP bayan sa ido kan hanyoyin da ake bi wajen kai wa 'yanta'addan kayayyaki.

Kazalika, waɗanda ake zargin sun amsa laifin kai abinci da sauran kayayyaki ga mayakan ISWAP da ke aiki a ƙauyen Kwatan Dowoshi a Ƙaramar Hukumar Kukawa, a cewar sanarwar. 

Jami'an tsaron sun gano kwalaye na biskit da madara da sabulu da garri da fitilu da wayoyin hannu da magungunan gargajiya da manyan wuƙaƙe da kuma kuɗaɗe a hannun waɗanda ake zargin, in ji sanarwar.

Haka kuma rundunar ta ce dakarunta na Bataliya ta 222 sun kama wasu mutane 20 da ake zargi 'yan’uwa mambobin ƙungiyar Boko Haram ne, ciki har da mata tara da maza biyu da kuma yara tara, a kan titin Gezuwa a Ƙaramar Hukumar Konduga ta jihar Borno.

An ruwaito cewa mutanen sun tsere daga yankinsu ne bayan hare-haren sojoji da aka ci gaba da kai musu, kana an mika su ga jami'an leken asiri na sojin Nijeriya don tantancewa da kuma ƙarin bincike.

A wani lamari na daban, majiyoyin soji sun ce an kashe mutane biyar da ake zargin 'yan ISWAP ne, ciki har da wani jami'in lafiya da aka bayyana sunansa da Usman Dan Fulani da ƙwararrun masu kera bama-bamai huɗu, a yayin suke koƙarin haɗa wani na’urar fashewa (IEDs) a karamar hukumar Marte ta jihar Borno.

Majiyoyin sun ce ana zargin ƙungiyar da haɗa abubuwan fashewa don kai hare-hare kan hanyoyin wucewar sojoji.