| Hausa
AFIRKA
1 minti karatu
Sudan ta ce ta kakkaɓo jirgi mara matuƙi na 'adawa' a jihar Blue Nile
Ma'aikatar Tsaron Sudan ta ce jirgi mara matuƙin na shawagi ne a saman jihar Blue Nile kusa da Kurmuk. Lamarin na zuwa ne yayin da ake zafafa yaƙi tsakani sojin ƙasar da rundunar RSF a faɗin kudu maso gabashin ƙasar.
Sudan ta ce ta kakkaɓo jirgi mara matuƙi na 'adawa' a jihar Blue Nile
Sojin Sudan ta zargi rundunar RSf da amfani da jirage mara matuƙa wajen kai hare-hare kan ababen more rayuwar fararen hula

Ma’aikatar Tsaron Sudan ta bayyana ranar Lahadi cewa ta harbo wani jirgi mara matuƙi na “adawa” a jihar Blue Nile da ke kudu maso gabashin ƙasar.
A wata sanarwar da ta wallafa shafinta na Facebook, ma’aikatar ta ce an aiko da jirgi mara matuƙin ne daga cikin ƙasar Ethiopia kuma ya yi shawagi ne a saman jihar Blue Nile, kusa da Kurmuk.
Babu tsokaci nan-take daga hukumomin Ethiopia game da lamarin.
Daga farko a wannan watan, Sojin Sudan ta ce ta harbo jirage mara matuƙa uku samfurin FH-95 a jihar North Kordofan a kudancin ƙasar.
Hukumomin Sudan da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil Adama sun zargi rundunar RSF da kai hare-hare kan ababen more rayuwa na fararen hula.

Baya ga Blue Nile da Darfur, jihohin Kordofan uku — North Kordofan da West Kordofan da kuma South Kordofan — sun fuskanci arangama tsakanin soji da rundunar RSF tun ranar 25 ga watan Oktoba na shekarar 2025.

Sudan na fama da yaƙi tsakanin sojin ƙasar da rundunar RSF tun watan Afrilun shekarar 2023, lamarin da ya kashe gomman dubban mutane tare da raba kimanin mutum miliyan 13 da gidajensu, in ji kiyasin Majalisar Ɗinkin Duniya da na ƙasashen duniya.