| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Mutane akalla 30 sun mutu sakamakon ruftawar wani babban wurin tara bola a Guinea
Tuni aka aika da ma'aikatan agajin gaggawa wani babban wuri tara bola da ya rufta a babban birnin Guinea bayan mamakon ruwan sama, lamarin ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
Mutane akalla 30 sun mutu sakamakon ruftawar wani babban wurin tara bola a Guinea
Ruftawar wani babban wuri tara bola ya kashe aƙalla mutane 30 a Guinea

Aƙalla mutane talatin ne suka mutu a babban birnin Guinea Conakry a ranar Lahadi bayan wani babban wurin tara shara ya rufta kan wasu gidaje da ke maƙotaka da wurin a yayin da aka shafe tsawon lokaci ana mamakon ruwan sama, a cewar gwamnatin ƙasar.

Kazalika mutum shida sun jikkata sakamakon wannan iftila’in wanda ya faru da misalin ƙarfe 2:00 na asuba (02:00 GMT) a unguwar Dar-es-salam da ke gundumar Bbessia a wajen babban birnin, in ji wata sanarwa ta gwamnati.

"An tura muhimman kayayyaki da masu aikin ceto don neman ƙarin gawawwakin da lamarin ya rutsa da su a ƙarƙashin tarkacen sharar," in ji sanarwar.

Firaminista Amadou Oury Bah ya ziyarci wurin da iftila’in ya faru, inda masu tonon ƙasa suke gudanar da aikin ceto.

An ɗauki matakai "don tabbatar da lafiyar waɗanda suka jikkata sakamakom lamarin" da kuma "taimaka wa waɗanda wannan mummunan iftila’i ya shafa," a cewar sanarwar ta gwamnati.

Mummunan Iftila'i

Kafin sanarwar da aka fitar a hukumance game da adadin mutanen da suka mutu, shugaban gundumar Lancine Sylla ya bayyana cewa, ana fargabar mutuwar mutane da dama sakamakon mummunan iftila’in.

"Mun fitar da gawawwaki 18 da aka kai su ɗakin ajiye gawa," in ji shi.

Ɗaya daga cikin jiga-jigan 'yan adawa na Guinea, tsohon firaminista Cellou Dalein Diallo, wanda ke gudun hijira a ƙasar waje, ya bayyana hatsarin a matsayin wani "mummunan bala'i da ya jefa mu cikin damuwa".

"Wannan bala'in abun damuwa ne domin sai da aka sanar da rufe wurin zubar da sharar a wannan Lahadi, 23 ga watan Agusta," kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Facebook.

"Yanzu ya rage wa hukumomin da suka dace su fito su bayyana yanayin da ya haifar da wannan bala'in, tare da samar da cikakken bayani, da kuma yin hukuncin da ya dace," in ji shi a saƙon da ya wallafa kafin sanarwar adadin mutanen da suka mutu.

A 'yan kwanakin nan, gwamnatin ƙasar Guinea ta ba da umarnin a kori mutanen da ke kusa da wurin saboda fargabar ruftawar wajen.

Gwamnatin Guinea na ƙarƙashin jagorancin Janar Mamadi Doumbouya wanda ya ke rike da mulki bayan juyin mulkin da ya auku a ƙasar a shekarar 2021 kafin a zabe shi a matsayin shugaban ƙasa a watan Disamba na shekarar 2025.