| Hausa
SIYASA
2 minti karatu
Maishari'ar Amurka ta soke umarnin Trump na haramta wa 'yan Nijeriya da 'yan ƙasashe 74 biza
Trump ya yi yaƙin neman zaɓe na shiga fadar White House ne bisa alƙawarin korar miliyoyin baƙi da ba a yi wa rijista ba kuma ya ɗauki wasu matakai tun da ya koma White House domin gaggauta tasa ƙeyar baƙi da kuma rage ƙetare kan iyakoki.
Maishari'ar Amurka ta soke umarnin Trump na haramta wa 'yan Nijeriya da 'yan ƙasashe 74 biza
Hukuncin alƙalin ya yi tarnaƙi ga matakin Trump na fatattakar baƙi daga ƙasar

Wata maishari'ar Amurka ta soke wani umarnin haramta biza ga ‘yan Nijeriya da ‘yan wasu ƙasashe 74 da ke son zaman dindinddin a ƙasar, lamarin da ya yi tarnaƙi ga matakin Trump na murƙushe ƙoƙarin baƙi na zama a ƙasar.

A wani hukuncin da ta yi ranar Jumma’a a Gundumar Kudanci ta New York, Maishari’a Jeannette Vargas ta bayyana manufar "a matsayin abin da ya saɓa wa doka" kuma ta ce Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya zarce "ikonsa na doka" wajen ba da umarnin.

Manufar, wadda ta fara aiki a watan Janairu, ta dakatar da ba da biza ga ‘yan ƙasashe 75 ciki har da ‘yan Afghanistan da Brazil da Masar da Iran da Iraƙi da Nijeriya da Somaliya da kuma Yemen.

A wancan lokacin, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce an ɗauki matakin ne "domin tabbatar da cewa baƙi daga ƙasashe da ke da hatsari sosai ba su yi amfani da tsarin jin-daɗin jama’a na Amurka ba ko kuma su zama masu tayar da hankalin jama’a"

Amma Vargas ta yanke hukuncin cewa an ba da umarnin da ya saɓa wa ƙa’ida ga jami’an ofisoshin jakadanci cewa su ƙi ba da biza bisa ƙasar da masu neman bizar suka fito kawai, ko ma sun gane cewa mai neman bizar ba haka yake ba.

Hukuncin na ranar Jumma’a ya soke duk wani matakin hana biza da aka ɗauka bisa wannan manufar kaɗai.

Gwamnatin za ta iya ɗaukaka ƙara a kan hukuncin, in ji kamfanin dillancin labaran AFP.