| Hausa
NIJERIYA
1 minti karatu
NDLEA ta kama wata tsohuwa mai shekara 101 da tabar wiwi a cikin garin alabo
A cewar NDLEA, matar mai shekaru fiye da 100 ta shaida wa masu bincike cewa ta shiga harkar sayar da miyagun kwayoyi baya gobara ta lalata shagonta na da take sayar da kayan abinci.
NDLEA ta kama wata tsohuwa mai shekara 101 da tabar wiwi a cikin garin alabo
NDLEA ta kama wata tsohuwa mai shekara 101 da tabar wiwi a cikin garin alabo da ya kai gram 90

Ma'aikatan Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) sun kama wata tsohuwa mai shekara 101 saboda zarginta da sayar da tabar wiwi a ƙauyen na Jihar Ogun.

An kama ta ne a ranar 15 ga Agustan 2026 da wani nau’in wiwi mai nauyin giram 90. hukumar ta ce dattijuwar tana sayar da tabar wiwi ɗin ne kaɗan-kaɗan.

Masu AlakaTRT Afrika - NDLEA ta kama ƙasurgumin mai safarar ƙwaya da mutum 5 kan kama ‘yan Nijeriya 3 da aka yi a Saudi

A cewar NDLEA, matar mai shekaru da fiye 100 ta shaida wa masu bincike cewa ta shiga harkar sayar da miyagun ƙwayoyi ne bayan gobara ta lalata shagonta na sayar da kayan abinci.

Ta bayyana cewa 'yarta, wacce ke zaune a jihar Legas ce take samar mata da wiwi duk bayan kwana huɗu don ta sayar wa abokan cinikayyarta a yankin da take.

Bayan kama ta da aka yi, Shugaban Hukumar NDLEA ta ƙasa, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya), ya ba da umarnin a ba da belinta kuma a ba ta shawara tare da gargaɗinta saboda tsufanta.

An kama 'yarta daga baya bisa zarginta da ta’ammali da kuma kasuwancin miyagun ƙwayoyi.