| Hausa
DUNIYA
2 minti karatu
Macron ya ce Faransa na fama da gobarar daji mafi muni da ba a taɓa ganin irinta ba
"Makonni masu zuwa za su kasance masu matuƙar wahala, kuma dole ne mu dage," a cewar Shugaban Faransa Emmanuel Macron.
Macron ya ce Faransa na fama da gobarar daji mafi muni da ba a taɓa ganin irinta ba
Jimillar jami'an kashe gobara 84 ne suka jikkata yayin da suke kokarin shawo kan gobarar.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce ƙasarsa tana fama da gobarar daji mafi muni "da ba a taɓa ganin irinta ba" kuma "makonni masu zuwa za su kasance masu matuƙar wahala" yayin da hukumomi ke ci gaba da ƙoƙarin shawo kan mummunar gobara a yankin kudu maso yamma.

"Makonni masu zuwa za su kasance masu matuaƙr wahala, kuma dole ne mu dage," in ji Macron yayin ziyarar da ya kai sashen ayyukan kashe gobara da ceto na ma'aikatar (CODIS) da ke Bordeaux a ranar Litinin.

Ya ƙara da cewa ba a taɓa ganin irin wannan mummunar gobara a Gironde ba "kwata-kwata."

Macron ya ce dole ne ƙasar ta ci gaba da ƙoƙarin kashe abin da ya bayyana a matsayin gobarar daji mafi muni a tarihi.

Masu AlakaTRT Afrika - Turai na babbakewa: Me muka sani zuwa yanzu?

Shugaban na Faransa ya gode wa jami’an kashe gobara da na farar-hula da ‘yansanda da na tsaro da sojoji da ma'aikatan kiwon lafiya, da ma’aikatan sa-kai da kuma manoma waɗanda suka taimaka wajen ci gaba da shawo kan lamarin.

Haka kuma, ya miƙa godiya ga ƙasashen Turai da suka taimaka wa Faransa, yana mai yabawa kan abin da ya bayyana a matsayin babbar hanya ta haɗin kai. 

"Na san rayuwa tana da wahala, ana cikin damuwa, an rasa amfanin gona, ga kuma man fetur na da tsada," in ji Macron. "Na san 'yan kwanakin nan sun kasance masu matuƙar wahala."

Macron ya yi ta'aziyya ga iyalan jami’an kashe gobara biyu da suka mutu a makon da ya wuce yayin da suke ƙoƙarin aikin kashe gobarar dajin, yana mai jajanta wa hukumar CODIS tare da gode wa jami'an agajin gaggawa saboda ci gaba da ƙoƙarinsu.

Ya ce nan gaba Faransa za ta sake dasa wa tare da farfaɗo da dazukanta ta wata hanya daban.

Gobarar dajin, wadda ta tashi a kusa da Saumos da ke yankin Gironde na Faransa a ranar Laraba ta ƙone kusan hekta 42,000 (kadada 103,784) kuma ta tilasta kwashe mutane fiye da 220,000 daga gidajensu.

Jimillar jami’an kashe gobara 84 ne suka jikkata yayin da suke ƙoƙarin shawo kan gobarar.

Kazalika, har yanzu gobarar tana ci gaba ci a yankin Haute-Corse, da Var da kuma Landes, yayin da hukumomi suka ce an shawo kan gobarar da ta tashi a yankin Hautes-Alpes.

Rumbun Labarai
CIA ta yi shakkar iƙirarin da Isra'ila ta yi kan shirin halaka Trump bayan taron NATO: rahoto
Za a fara shari'ar wanda ake zargi da hannu a kashe Tupac Shakur a Amurka
‘Yan Bangladesh akalla 16 sun mutu sakamakon gobara a masana'antar yin kujeru ta Saudiyya
Gobarar daji a jihar Washington ta Amurka ta tilasta wa dubban mutane tserewa
Jirgin yaƙin Amurka samfurin F-35 ya faɗi kusa da wani sansanin soji
Tarayyar Turai ta yi kira da a zartar da umarnin Kotun ICC na kamo Netanyahu
Turai na babbakewa: Me muka sani zuwa yanzu?
Faransa da Sifaniya na fama da mummunar gobarar daji
Yadda kujerar Firaministan Birtaniya ke komawa tamkar kujerar aski
Trump ya ce ba za a yi yarjejeniyar nukiliya da Saudiyya ba sai ta amince da gyara alaƙa da Isra'ila
Trump ya tarbi gawawwakin sojojin Amurka da aka kashe a yaƙin Iran
Trump ya amince da yarjejeniyar shirin nukiliya na farar-hula da Saudiyya — Rahoto
Sabon Firaministan Birtaniya Burnham ya yi alƙawarin rage tsadar rayuwa
Netanyahu ya fusata Trump bayan ya caccaki shirin Amurka na sayar wa Turkiyya F-35: Rahoto
Ana fargabar mutuwar 'yan ƙabilar Rohingya fiye da 500 bayan kifewar jiragen ruwa a gaɓar Myanmar
Masu ceton dabbobi na taimaka wa tsuntsaye tsira daga bazara mai zafi
Ƙirkirarriyar Basira, ƙarfin intent da ƙa’idojin aikin jarida
Yawan masu kamuwa da cutar kansa na iya kusan ninkuwa nan da shekarar 2050
Mai tsaron bayan Argentina ya ce alƙalan wasan Gasar Kofin Duniya 'na aiki mai kyau'
An kona gini mai kama da masallaci a Arewacin Ireland  a yayin da ‘yansanda ke gudanar da bincike