| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da shirye-shiryen ayyukan Bankin Duniya na dala biliyan 3.05
An shirya ayyukan ne da zummar tabbatar da cewa alkhairin sauye-sauyen sun kai ga mutane ta hanyar inganta rayuwa da kuma damar samun muhimman hidindimu.
Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da shirye-shiryen ayyukan Bankin Duniya na dala biliyan 3.05
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya ƙaddamar da ayyukan Bankin Duniya uku da kimar kudinsu ya kai dala biliyan $3.05 domin ƙarfafa shirin kiyaye zamantakewa da ƙwarewar mutane da kuma tallafi ga al’ummomi masu rauni a faɗin ƙasar.

An shirya ayyukan ne da zummar tabbatar da cewa alkhairin sauye-sauyen sun kai ga mutane ta hanyar inganta rayuwa da kuma damar samun muhimman hidindimu.

A cikin wani muhimmin jawabin taro da ministan kuɗi, Taiwo Oyedele, ya gabatar a madadinsa, Shugaba Tinubu ya bayyana shirye-shiryen a matsayin muhimman ginshiƙai na manufar gwamnatinsa ta Renewed Hope Agenda, yana mai cewa “an tsara ayyukan ne domin tabbatar da cewa ribar sauyin da ake yi wa tattalin arziƙin ƙasar sun samar da ingantacciyar rayuwa ga ‘yan Nijeriya.”

Ya ce shirye-shiryen za su faɗaɗa tallafi ga ƙananan manoma da ƙananan da matsakaitun masana’antu da ƙarfafa cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko da inganta koyarwa na sharan fage a makarantin gwamnati da kuma tallafa wa malamai.

Za su kuma haɓaka fayyace gaskiya a aikin gwamnatin a matakin mazaɓu da kuma samar da ababen more rayuwa da hanyoyinsa samun kuɗaɗen biyan buƙatu da kuma muhimman hididimu ga ‘yan gudun hijira da al’ummomin da ke karɓar baƙuncinsu.

Shugaban ya bayyana cewa ayyukan sun kasance tsari na ƙasa na rage talauci da inganta uwar kuɗi da ƙwarewar mutane da kuma juriyar mutane.

Ya jaddada cewa gwamnatin ta jajirce wajen tabbatar da cewa farfaɗowar tattalin arzikin ya kai ga ko wane iyali.

Bugu da ƙari, Shugaba Tinubu ya ce ; “Gyare-gyaren tattalin arzikin Nijeriya sun riga sun fara samar da sakamako na gari, inda kimar tattalin arziƙi a ma’aunin GDP ya ƙaru da kashi 11.2 cikin 100 da kuma ƙarin kudin shiga na kusan kashi 10 cikin 100 na dalar Amurka a cikin shekarar da ta gabata, yayin da ajiyar kudin Nijeriya a ƙetare ta zarce dala biliyan $50 yayin da hawhawar farashi ya ragu sosai daga ƙololuwar da ta kai a shekarar 2024.”

Ya kuma bayyana cewa gwamnatin ta faɗaɗa shirin raba tallafin kuɗi zuwa iyalai masu rauni miliyan 15, inda ta fitar da kimanin ‘yan Nijeriya miliyan 7.5 daga talauci.

Shugaban ya bayyana cewa shirye-shiryen sun dace da manufofin ci-gaban na gwamnatin shugaban, waɗanda suka mayar da hankali a kan faɗaɗa hanyoyin samun kuɗi ga tattalin arziki da ƙarfafa gwamnatoci a matakan ƙasa da gwamnatin tarayya a wani ɓangare na burin gwamnatin na gina tattalin arziki mai kimar dala tirliyan 1 nan da shekarar 2030.

Shugaban na Nijeriya ya yi kira a gwamnatocin jihohi da ƙananan hukumomi da abokanan aiki na harkar ci-gaba da kuma aiwatar da shirye-shiryen yadda ya dace, yan amai cewa nasararsu ya dangane da kan haɗin kai mai girma a dukkan ɓangarotin gwamnati.

Rumbun Labarai
Gwamnonin Arewa maso-gabashin Nijeria sun yi shelar kafa kamfanin jiragen sama na yanki
Tinubu ya ceci Nijeriya daga wargajewa, in ji Kashim Shettima
Yawan iskar gas ɗin da Nijeriya ke samarwa a cikin gida ya ɗara ƙafa biliyan 2
Mutfwang ya gana da Tinubu, ya ce an fara gurfanar da masu kai hare-hare a Filato
'Yansandan Nijeriya sun ceto mutane 10 daga cikin 'yan NYSC da aka yi garkuwa da su a jihar Imo
Nijeriya: Mutane uku sun mutu a turmutsitsin rabon tallafin kuɗi a Jihar Neja
Ranar 'Yancin Kai a Nijeriya: Sauye-sauyen da muke yi za su haifar da sakamako mai kyau - Tinubu
Dubban fasinjojin Kano da suka bi Saudi Airline sun koka cewa kayansu sun maƙale a Saudiyya
Rundunar Sojin Nijeriya ta ƙaddamar da motocin yaƙi masu sulke da bataliyar soji uku a jihar Kebbi
'Yansandan Nijeriya sun gano ƙoƙon kawuna 28 a wani daji a Jihar Abia
Kotun Nijeriya ta umarci NMDPRA ta bai wa A.A Rano, AYM Shafa da Matrix lasisin shigo da fetur
An sace fiye da mutum 80 a cikin mako biyu a arewacin Nijeriya
‘Yan Nijeriya fiye da 67,000 sun amfana da shirin ba da lamuni ga ƙananan masana'antu – Tinubu
Tinubu yana nan lafiya, zai koma Nijeriya a makon nan: Fadar Shugaban ƙasa
Kwalara ta kashe wasu fursunoni a gidan gyaran hali na Kurmawa da ke Kano
Sojojin Nijeriya sun kama mutum uku da ake zargi da yi wa ‘yanta’adda aikin masinja a Katsina
An sake harbe wani ɗan Nijeriya har lahira a Afirka ta Kudu
Nijeriya ta buƙaci a bai wa Afirka kujeru biyu na dindindin a Kwamitin Tsaro na MƊD
Nijeriya da Amurka sun ƙulla yarjejeniyar biliyan $700 a ɓangaren haƙar ma'adinai
Ƙungiyar Amnesty International ta soki gwamnatin jihar Kano a Nijeriya kan musguna wa ‘yan adawa