| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Dakarun Nijeriya sun kuɓutar da mutum 12 da aka yi garkuwa da su a jihohin Katsina da Benue
Kazalika sojojin sun samu sun ƙwato shanu 56 tare da kashe wasu daga cikin waɗanda ake zargi da kasancewa cikin masu garkuwa da mutanen.
Dakarun Nijeriya sun kuɓutar da mutum 12 da aka yi garkuwa da su a jihohin Katsina da Benue
Wasu daga cikin makaman da sojojin suka ƙato daga 'yan bingida a jihar Binuwe

Dakarun Nijeriya sun yi nasarar kuɓutar da mutum 12 da aka yi garkuwa da su a jihohin Kastina da Benue duk a arewacin ƙasar.

Wata sanarwa da jami’in watsa labarai na rundunar Operation Fansan Yamma mai yaƙi da rashin tsaro a arewa maso yammacin ƙasar, Laftanal Kanar Aliyu Danja ya fitar ranar Jumm’a ta ce dakarun sun yi nasarar ceto mutum tara da aka yi garkuwa da su ne a ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina.

“A ɗaya daga cikin ayyukan, dakarun ɓangare na 2 da ke kan sintiri na yaƙi sun ceto mutum tara da aka yi garkuwa da su, ciki har da mata uku da maza huɗu da ƙanan yara biyu a ƙaramar hukumar Faskari,” in ji sanarwar.

Kazalika sojojin sun samu sun ƙwato shanu 56 tare da kama wani daga cikin waɗanda ake zargi da kasancewa cikin masu garkuwa da mutanen.

Masu AlakaTRT Afrika - Fiye da mutum 1,000 ne suka tsere wa hare-haren 'yanbindiga a jihar Benue ta Nijeriya

“Bincike na farko-farko ya nuna cewa ‘yanta’adda sun yi garkuwa da waɗanda lamarin ya rutsa da su ne ranar 9 ga watan Yuli na 2026 a kan hanyar Tsafe zuwa Kuchere a ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara,” in ji Laftanar Kanar Danja.

Waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin sun bayyana cewa sun tsere ne daga dabar ‘yanta’addan yayin da waɗanda suka kama su ɗin ke barci, kafin sojoji su ci karo da su kuma su ceto su, in ji sanarwar da rundunar sojin Nijeriya ta wallafa a shafinta na X.

Kazalika rundunar sojin Nijeriyar ta wallafa wata sanarwar ta kuɓutar da mutum uku da aka yi garkuwa da su a jihar Benue tare da kashe mutum biyu da ake zargi da ta’addanci.

Sanarwar da muƙaddashin jami’in watsa labaran rundunar Operation Whirl Stroke, Laftanar Ahmad Zubairu, ya fitar ta ce rundunar ta cim ma nasarar ne sakamakon samamen da ta kai bisa bayanan sirri a ƙaramar hukumar Katsina-Ala ta jihar Benue.

Samamen wanda aka fara da misali ƙarfe 03:00 na ranar 16 ga watan Yuli kuma aka kammala shi ranar 17 ga watan Yuli na 2026, ya faru ne yayin da dakaru su fito ta Takum a jihar Taraba zuwa gundumomin Tse Togo da Utenge da ke tsallaken kogin River Yooyo a sansain Orter Camp, inda ‘yanta’addan ke zama, in ji sanarwar.

“Yayin aikin, dakaru sun yi arangama da masu aikata laifukan a cikin wata zazzafar musayar wuta inda suka kassara biyu daga cikinsu,” in ji sanarwar.

Ta ƙara da cewa dakarun su ceto Mista Nyityo Abraham, wani malamin makaranta da Mista Uzuegwu Chukwuemeka Decency, wani mai sayar da kayayyakin inji da Mista Terhember Tavarshima, wani manomi yayin da sauran waɗanda aka yi garkuwa da suka tsere yayin bata-kashin.

Ababen da sojojin suka ƙwace a hannunsu sun haɗa da wani bindiga samfurin AK-47 da wata bindiga samfurin G3 da wata ƙaramar bindiga da ƙwanson harsasan AK-47 guda 19 da wata na’urar POS da sauransu.