Ma'aikatar Lafiya ta Turkiyya ta buɗe asibitoci na musamman don taimakawa matasa su daina shan taba sigari da kuma kawar da maitar sinadarin nicotine tun suna ƙanana.
Masana kiwon lafiya sun yi gargaɗin cewa samartaka lokaci ne mai matuƙar hatsari ga samun halayyar maitar nicotine saboda dalilai da suka haɗa da zumudi, matsin lamba na sa’o’i, tasirin kafofin sada zumunta, rashin fahimta game da hatsarin lafiya da kuma sauƙin samun samfuran nicotine na zamani.
Shan sinadarin nicotine a lokacin ƙuruciya da samartaka na iya yin mummunan tasiri ga ci gaban kwakwalwa, wanda hakan zai iya haifar da matsaloli na dogon lokaci mayar da hankali, koyo, ƙwaƙwalwa da kuma sarrafa motsin rai.
Shan taba da wuri yana ƙara yiwuwar kamuwa da cutar shan barasa da sauran jarabtuwa da shan ƙwayoyi daga baya a rayuwa.
Asibitocin Dakatar da Shan Sigari na Matasa na Ma'aikatar Lafiya suna da nufin samar wa matasa auna lafiya, shawarwari da magani da suka dace da buƙatunsu na halitta, tunani da zamantakewa.
Asibitocin suna ba da tallafi bisa ga halin da aka shaida yayin aiki tare da likitocin tabin hankali na yara da matasa, masana ilimin halayyar ɗan adam, ma'aikatan zamantakewa da sauran ƙwararru idan ya zama dole.
Jami'an kiwon lafiya sun ce shiga tsakani da wuri yana da muhimmanci ba wai kawai don hana shan taba ba, har ma don dakatar da dogaro da nicotine da rage hatsarin lafiya a nan gaba.
Asibitocin za su yadu a fadin kasar
Sabbin asibitocin sun fara aiki a watan Yunin 2026 kuma a halin yanzu suna ba da ayyuka a cibiyoyi bakwai a Agri, Ankara, Bursa, Canakkale, Corum da Kutahya.
Ma'aikatar tana shirin faɗaɗa ayyukan a faɗin ƙasar ta hanyar ƙara yawan cibiyoyin da kuma samar da ayyukan daina shan taba ga matasa a kowane lardi.
A halin yanzu Turkiyya tana da asibitoci 1,600 na daina shan taba waɗanda ke yi wa mutane hidima a duk faɗin ƙasar ya zuwa ranar 9 ga Yulin 2026.
Ma'aikatar ta kuma shirya ka’idoji a asibitocin ga likitocin da ke aiki a sabbin cibiyoyin matasa.
Batun shekaru 18
A cewar ƙungiyar ‘Green Crescent ta Turkiyya’ (Yesilay), kashi 62.9 cikin 100 na masu shan taba a Turkiyya sun fara sha ne kafin su kai shekara 18, inda matsakaicin shekarun da suka fara shan taba ya kama shekara 16.9.
Yawan shan taba da wuri ya fi yawa a tsakanin samari, da kashi 68.6 cikin 100, idan aka kwatanta da kashi 54.2 cikin 100 a tsakanin 'yan mata, a cewar rahoton Yesilay na shekarar 2025 bisa ga bayanai daga Cibiyoyin Ba da Shawara na ‘Green Crescent (YEDAM)’.
Bincike da aka buga a mujallar Yesilay mai suna Addicta: Jaridar Turkiyya kan Jarabtar SHan Taba ya gano cewa kashi 21.5 cikin 100 na ɗaliban makarantun sakandire da na sana'a da fasaha suna shan taba sigari ta gargajiya, yayin da kashi 19.6 cikin 100 ke amfani da sigarin lantarki, wanda hakan ya nuna karuwar amfani da kayayyakin shan taba a tsakanin matasa.
Jami'an lafiya sun kiyasta cewa cututtukan da suka shafi shan taba sigari na haifar da mutuwar kusan mutane 100,000 a kowace shekara a Turkiyya, wanda hakan ya sanya shan taba ya zama ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke haifar da mutuwa a ƙasar kuma ya nuna muhimmancin ƙoƙarin rigakafin da wuri.



















