| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Sojojin Nijeriya sun kama 'yan ƙasashen waje 24 a wani samame a Jihar Legas
Rundunar ta ce an gudanar da samamen ne tare da haɗin gwiwar jami'an ƙungiyar sa-kai ta Vigilante Group, bayan samun sahihan bayanan sirri kan kasancewar wasu baƙin-haure da ba su da takardun izinin zama a yankin.
Sojojin Nijeriya sun kama 'yan ƙasashen waje 24 a wani samame a Jihar Legas
Sojojin Nijeriya sun kama 'yan kasashen waje 24

Dakarun Bataliya ta 65 ta Rundunar Sojin Nijeriya sun kama 'yan ƙasashen waje 24 a wani samame da suka kai wani wurin da ake zargin mafakar wasu mutane ne a ƙaramar hukumar Epe ta Jihar Legas, a wani ɓangare na ƙoƙarin da ake yi na yaƙi da aikata laifuka da kuma shige da fice ba bisa ƙa'ida ba.

Rundunar ta ce an gudanar da samamen ne tare da haɗin gwiwar jami'an ƙungiyar sa-kai ta Vigilante Group, bayan samun sahihan bayanan sirri kan kasancewar wasu baƙin-haure da ba su da takardun izinin zama a yankin.

A cewar rundunar, dakarunta sun kai samame wani katafaren fili mai katanga da ke yankin Imokun, a kan titin Odo-Noforija/Poka da ke Epe, inda suka kama maza 15 da mata tara.

Binciken farko ya nuna cewa waɗanda aka kama 'yan ƙasashe shida ne na Yammaci da Tsakiyar Afirka. Sun haɗa da 'yan Kamaru 10, 'yan Togo shida, 'yan Côte d'Ivoire uku, 'yan Jamhuriyar Benin uku, ɗan Burkina Faso ɗaya da kuma ɗan Guinea-Bissau ɗaya.

Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike domin tabbatar da matsayin shigowarsu Nijeriya, dalilin zamansu a ƙasar, da kuma ko suna da hannu a wata haramtacciyar harka.

Haka kuma, jami'an tsaro na ƙoƙarin gano tare da yi wa mai gidan da aka kama mutanen tambayoyi domin ƙarin haske kan yadda suka zauna a wurin da kuma irin ayyukan da suke gudanarwa.

Rundunar ta ce a ranar 16 ga Yulin 2026 ta miƙa dukkan waɗanda aka kama ga Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya (NIS), reshen Jihar Legas, domin ci gaba da bincike da tantancewa tare da ɗaukar matakan da dokokin shige da fice suka tanada.

Babban Kwamandan Runduna ta 81 ta Sojin Najeriya, Manjo Janar Adebayo Babalola, ya yaba wa dakarun bisa ƙwarewa da nuna ƙwazo wajen gudanar da aikin.

Ya kuma umarce su da su ci gaba da ƙara zage damtse wajen yaƙi da masu aikata laifuka, baƙin-haure ba bisa ƙa'ida ba da sauran barazanar tsaro, tare da jaddada kudurin rundunar na ci gaba da aiki tare da sauran hukumomin tsaro domin tabbatar da zaman lafiya da kare lafiyar al'umma a yankunan da ke ƙarƙashin kulawarta.