Ƙasar Uruguay tana shirin ɗauko tsohon gwarzon ɗanwasan tawagarta, Diego Forlan wanda tsohon ɗanwasan gaban Manchester United ne, don ya zama sabon kocinta.
Wannan na zuwa ne bayan da Uruguay ta gaza taka rawar gani a gasar Kofin Duniya da ake kammalawa a Amurka, Canada, da Mexico, inda aka fitar da ita tun a zagayen rukuni.
Ana sa ran Diego Forlan zai maye gurbin Marcelo Bielsa, tsohon kocin da ya ajiye aiki bayan dawowarsu daga Kofin Duniya na FIFA 2026.
Diego Forlan ɗaya ne cikin ‘yanwasan tawagar Uruguay mafi shuhura, kuma sanda yana ɗanwasa ya jagoranci tawagar Uruguay zuwa wasan dab da na ƙarshe na Kofin Duniya na 2010.
Bayan nan kuma ya lashe Kofin Copa America na 2011 tare da tawagar.
Rahotannin na cewa tuni an shirya ganawa tsakanin Forlan da shugaban hukumar ƙwallo ta Uruguay, Ignacio Alonso, don kammala tataunawa kan ba shi aiki jagorancin tawagar.
Bisa yadda aka tsara, Forlan zai fara karɓar jagorancin tawagar Under-20 ta ƙasar yayin gasar Kofin Duniya na ‘yan-ƙasa da shekaru 20 a Azerbaijan da Uzbekistan.
Zai riƙe wannan muƙami yayin da kuma yake riƙon-ƙwarya na babbar tawagar ƙasar har zuwa Maris ɗin 2027. Daga nan za a bar ƙofa a buɗe ga Forlan da ya zama kocin dindindin.


















