| Hausa
NIJERIYA
1 minti karatu
Wata kotu a Kano ta hukunta wanda ya tallata wiwi a intanet da zaman yari na shekaru 7
Matashin mai suna Ashiru Idris, ɗan shekara 28 zai fara zaman gidan yari daga ranar da aka yanke masa hukuncin.
Wata kotu a Kano ta hukunta wanda ya tallata wiwi a intanet da zaman yari na shekaru 7
Kotun ba ta ba wa mai laifin zaɓin tara ba.

Babbar kotun tarayyar Nijeriya mai zama a jihar Kano ta yanke wa wani mai shekaru 28 hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru bakwai, bayan kama shi da laifin tallata wiwi a intanet.

Hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasar, NDLEA, reshen jihar Kano ce ta sanar da wannan a wata sanarwa daga magatakardar ƙungiyar, Sadiq Muhammad Maigatari.

Alƙalin babbar kotun tarayyar, Mai Shari’a S.M. Shuaibu ne ya yanke hukuncin ranar 14 ga Yulin 2026, kan mai laifin mai suna Ashiru Idris, ɗan shekaru 28, ba tare da ba shi zaɓin biyan tara ba.

Sanarwar ta nuna cewa hukuncin kotun zai fara aiki ne daga ranar yankewa.

NDLEA ta ce a ranar 22 ga Afrilun 2026 ne jami’an hukumar na reshen jihar Kano suka kama mai laifin, bayan yaɗuwar wani bidiyo a soshiyal midiya da ya nuna shi yana tallata tabar wiwi.

Hukumar ta bayyana hukuncin a matsayin babban kashedi ga masu yaɗa halayyar ta’ammuli da sayar da miyagun ƙwayoyi.

Sannan ta yi kira ga jam’a da su mara wa yunƙurinta na yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi, ta hanyar ba da ƙwararan bayanai ga hukumomin tsaro.