Rundunar 'Yansandan Nijeriya reshen Jihar Kogi ta ce tana ƙara ƙaimi wajen ceto shugaban wata makaranta, wani jami'in wucin-gadi na Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandare ta Kasa (NECO) da kuma wasu ɗalibai da ake zargin 'yanbindiga sun yi garkuwa da su yayin wani hari da suka kai a wata makarantar sakandare a Ƙaramar Hukumar Dekina ta jihar.
Kakakin rundunar, ASP Saliu Oyiza Afusat, ta ce gamayyar jami'an tsaro da suka haɗa da 'yansanda, sojoji, 'yan bijilanti da mafarauta sun ƙaddamar da aikin bincike da ceto, inda suke ci gaba da bincike a dazukan da ke kusa domin gano masu garkuwar.
Ta ƙara da cewa an riga an ceto ɗaya daga cikin ɗaliban da aka sace, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ceto sauran mutanen da aka yi garkuwa da su.
An sace mutanen ne a ranar Talata lokacin da wasu 'yanbindiga suka kai hari Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Opada-Olowa, inda ɗalibai ke rubuta jarrabawar NECO. Maharan sun yi garkuwa da shugaban makarantar, Mista Nyada Daniel, wani jami'in wucin-gadi na NECO mai suna Mista Solomon Audu, da kuma ɗalibai huɗu.
Mazauna yankin sun ce maharan sun shiga wurin da misalin ƙarfe 2:00 na rana suna harbe-harbe domin tsoratar da jama'a kafin su kutsa cikin harabar makarantar. Harin ya sa ɗalibai da mazauna yankin suka rika gudun neman tsira.
Wani mazaunin yankin mai suna Ademu ya ce ɗan uwansa ya tsira ne bayan ya yi tsalle ta tagar aji a lokacin da ya hango 'yanbindigar. Ya ce da dama daga cikin ɗaliban sun riga sun tafi gida bayan sun kammala jarabawarsu, lamarin da ya taimaka wajen rage yawan waɗanda aka sace.

Wani mazaunin yankin, Sunday Alkali, ya ce wasu matasa a cikin al'ummar sun yi yunƙurin tunkarar maharan, amma suka ja da baya bayan da suka fara harbe-harbe. Ya ƙara da cewa bayan harbin ya lafa ne mazauna yankin suka gano cewa an kai hari makarantar, inda suka tarar da takardun jarabawa a warwatse cikin azuzuwa da harabar makarantar.
Majiyoyin al'umma sun ce daga bisani masu garkuwar sun tuntubi wasu daga cikin iyalan waɗanda aka sace, inda suka nemi kuɗin fansa masu yawa domin a sako su.
Gwamnatin Jihar Kogi ta ce jami'an tsaro daga rundunar soji, 'yansanda, Hukumar DSS, rundunar 'yan bijilanti ta jihar, mafarauta da sauran hukumomin tsaro an tura su yankin. Ta tabbatar wa al'umma cewa ana yin duk mai yiwuwa domin ceto sauran waɗanda aka sace cikin ƙoshin lafiya tare da kama waɗanda suka aikata harin.


















