| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Nijeriya ta zo ta farko a duniya a tagomashin kasuwar hannun-jari
Nijeriya na cin moriyar haɓakar madafan tattalin arziƙi, sakamakon aiwatar da sauye-sauye da ƙaruwar farashin ɗanyen mai a duniya, da kuma haɓakar darajar kuɗi a kasuwar musaya.
Nijeriya ta zo ta farko a duniya a tagomashin kasuwar hannun-jari
Bloomberg ta duna jimillar kasuwannin hannun jari 92 a duniya.

Kasuwar hannun-jari ta Nijeriya, NSE, ta zama kasuwa mafi tagomashi a duk duniya a wannan shekara, bisa ƙididdigar dala da mujallar Bloomberg ta yi kan kasuwannin hannun-jari 92 a duniya.

Wannan ci-gaba wata babbar alama ce da ke nuna yadda Nijeriya ke samun ƙaruwar ingancin manufofin tattalin arziƙin ƙasa, sakamakon sauye-sauyen da gwamnatin ƙasar ke gudanarwa a halin yanzu.

A cewar bayanan da Bloomberg ta bibiya game da ƙwazon kasuwannin hannun jari, daga farkon shekarar nan Nijeriya ta samar da kashi 67 na riba a lissafin dalar Amurka, sama da Koriya ta Kudu mai kashi 66.

Masu AlakaTRT Afrika - Naira da hannayen-jari Nijeriya sun faɗi sakamakon barazanar da Trump ya yi ta kai hari ƙasar

Nijeriya na cin moriyar haɓakar madafan tattalin arziƙi, sakamakon aiwatar da sauye-sauye da ƙaruwar farashin ɗanyen mai a duniya, da kuma haɓakar darajar kuɗi a kasuwar musayar kuɗi.

Bugu da ƙari, akwai tagomashin da kuɗin kasar, naira ya samu inda ya ɗaga da kashi 4 kan dalar Amurka tun daga watan Janairu, wanda ya kyautata yawaitar masu zuba jari daga waje.

Idan aka duba rukunin hannayen jarin da suka taimaka wajen wannan cigaba, akwai tarin bankuna da kamfanonin inshora da suka samu tagomashi mai girma.

Misali, kamfanin Fortis Global Insurance Plc ya zamo wanda ya fi kowanne ƙwazo, inda ya kawo ribar kusan kashi 1,400 a lissafin dala a wannan shekara.