| Hausa
TURKIYYA
1 minti karatu
Matar shugaban Turkiyya Emine Erdogan ta tuna da ranar murƙushe yunƙurin juyin mulkin 15 ga Yuli
Emine Erdogan ta ce murƙushe yunƙurin juyin mulkin ‘wata jajircewa ce da ta bijiro bisa kishin ƙasa da kuma ƙwazo marasa iyaka’.
Matar shugaban Turkiyya Emine Erdogan ta tuna da ranar murƙushe yunƙurin juyin mulkin 15 ga Yuli
Matar shugaban Turkiyya Emine Erdogan ta halarci bikin buɗe ɗakin karatu a wata makaranta a Istanbul ranar 14 ga Fabariru, 2026.

Matar shugaban ƙasar Turkiyya Emine Erdogan ranar Laraba ta ce yunƙurin juyin mulkin ranar 15 ga watan Yulin 2016, wanda aka murƙushe wata alama ce ta jajircewar ƙasar Turkiyya da yin tsayin-daka, inda ta jinjina wa waɗanda suka kare dimokuraɗiyya.

A wani saƙo da ta wallafa a shafin sada zumunta na Turkiyya NSosyal domin tunawa da Ranar Dimokuraɗiyya da Haɗin Kan Ƙasa wadda aka yi wa take da cewa #NasaraTamuCe wato #VictoryIsOurs a Turancin Ingilishi, Emine Erdogan ta ce ranar 15 ga Yuli "wani suna ne na jarumta da ta bijiro bisa kishin ƙasa da ƙwazo marasa iyaka."

"A wancan daren, gwarazanmu, waɗanda suka kasance haske maganin duhu, suna cikin zukatanmu kuma sun zama wata murya ta jajircewar ƙasa da kuma kare martaba da ‘yancinmu," in ji ta.

Matar shugaban Turkiyya ta ce fafutuka da sadaukarwar da aka yi wajen kare dimokuraɗiyya za su kasance “a zukatan ƙasarmu har abada."

Kazala ta jinjina wa waɗanda suka rasa rayukansu da waɗanda aka jikkata a lokacin yunƙurin juyin mulkin.

“Ina jinjina wa shahidai na ranar 15 ga Yuli tare da tunawa da gwarazan dakarunmu da yi musu godiya,” a cewarta.