Dakarun Operation Hadin Kai da ‘yansandan Nijeriya sun daƙile wani yunƙurin sace ɗalibai da ‘yanta’addan Daesh suka yi a makarantar sakandaren ‘yanmata ta Gwamnatin Tarayya (FGGC) a Monguno, jihar Borno.
Mohammed Goni, muƙaddashin jami’in watsa labaran rundunar Operation Hadin Kai, ne ya tabbatar da aukuwar lamarin ranar Lahadi, yana mai cewa sojojin sun kuɓutar da ɗalibai 46 a makarantar.
‘Yanta’addan sun far ma makarantar ne da misalin ƙarfe 1:30 na tsakar dare ranar Asabar bayan sun shiga wurin da taimakon wasu da suka haɗa baki da su, in ji sanarwar da kyaftin Mohammed Goni ya fitar.
Goni ya ce ɗalibai daga Kwalejin Kimiyya da Fasa ta Tarayya da ke Monguno ne ke amfani makarantar FGGC ɗin na wucin-gadi a lokacin da ‘yanta’addan suka kai harin.

Ya ƙara da cewa wasu daga cikin ɗaliban sun mutu a lokacin da harsasai na ‘yanta’addan da ke tserewa suka same su yayin musayar wuta.
Babu tabbacin ko ɗaliban da suka rasu ‘yan makarantar FGGC Monguno ne ko kuma ‘yan Kwalejin Kimiyya da Fasahar.
Sanarwar ta ce dakarun soji sun yi arangama da ‘yanta’addan inda suka ci ƙarfinsu lamarin da ya hana su ci gaba da aika-aikarsu.
Kazalika sanarwar ta ce babu ɗalibin da ‘yanta’addan suka sace.






















