| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Trump ya ce Amurka za ta kai hari kan tashoshin wutar lantarki da gadoji na Iran a makon gobe
Shugaban Amurka ya yi gargadin cewa Iran na iya fuskantar ƙarin hare-hare, ya kuma kara cewa za a kai hari kan muhimman kayayyakin more rayuwa idan Tehran ba ta koma kan teburin tattaunawa ba.
Trump ya ce Amurka za ta kai hari kan tashoshin wutar lantarki da gadoji na Iran a makon gobe
Trump ya yi alƙawarin kai hari kan hanyoyin samar da makamashi na Iran da manyan gadoji idan Tehran ba ta yi sulhu

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi gargadin cewa hare-haren da ake kai wa Iran za su ci gaba da tsananta a cikin kwanaki masu zuwa, yana mai gargadin cewa idan har Tehran ta ki komawa kan teburin tattaunawa, Amurka za ta soma kai hari kan tashoshin wutar lantarki da gadoji na ƙasar a mako mai zuwa.

‘‘Za mu kai musu hare-hare sosai, za mu kai hari kan duk wani abu da suke da shi a teku da kuma gabar tekunsu… Za su ci gaba har sai na ce ya isa," a cewar Trump a yayin wata hira da kafar wata labarai ta Fox News ta yi da shi.

Yayin da aka tambaye shi ko yana da shirin kai hari kan cibiyoyin makamashin Iran, Trump ya ba da amsa kamar haka: "Zan bar wuraren makamashi a ƙarshe, amma dai za mu kai hare-hare kan cibiyoyin makamashin".

Masu AlakaTRT Afrika - Vance ya tafi Switzerland, yayin da wakilan Iran suka isa don zuzzurfar tattaunawar zaman lafiya



"Za mu kai musu hare-hare cikin daren yau sosai. Haka kuma za mu kai musu hare-hare a daren gobe. Za mu kai musu hari a daren da zai biyo baya, sannan mako mai zuwa zai yi musu muni sosai, domin a mako mai zuwa ne za mu mayar da hankali kan tashoshin wutar lantarki.

A mako na gaba kuma za a kai hari a gadoji. Za mu lalata dukkan tashoshin wutar lantarkinsu. Za mu lalata dukkan tashoshin wutar lantarkinsu, sai dai idan sun hau teburin tattaunawa," in ji shi.

An dakatar da kudin fito na kayayyaki

Tun da farko, Trump ya yi watsi da bukatar ƙarbar kashi 20 cikin 100 na duk wasu kayayyaki da aka wuce da su ta Mashigar Hormuz, maimakon haka ya zaɓi tabbatar da yarjejeniyar cinikayya da saka hannun-jari kan ƙasashen Gulf.

Sauyin ya biyo bayan kwana guda da Trump ya ba da shawarar ƙarɓar kashi 20 cikin 100 na kuɗin fito don kare hanyar ruwan mai mahimmanci.

"Bisa tattaunawa mai muhimmaci da shugabannin Gabas ta Tsakiya, na yanke shawarar maye gurbin kashi 20 cikin 100 na kuɗin fito da Amurka za ta biya da Yarjejeniyar Cinikayya da Zuba Jari da ƙasashen Gulf daban-daban za su yi a Amurka," kamar yadda Trump ya wallafa a shafinsa na Truth Social ranar Talata.

Trump bai fayyace wani alƙawari na kai-tsaye da ƙasashen Gulf suka yi ba, kawai ya mayar da hankali ne kan "zuba jari mai yawa, sannan a lokaci guda,’’ a cewarsa ‘‘zai yi musu kyau sosai, da kuma makomarsu".

Trump ya ce ya yi imanin cewa Iran ba ta da "zaɓi" sai dai ta yi yarjejeniya, inda ya ƙara da cewa wakilan Amurka suna kan tuntuɓar jami'an Iran, ko kamar awa ɗaya kafin hirar.

"Suna son yin yarjejeniya... Ya kamata ku yi yarjejeniya. Ba za ku bar kowa ba," in ji Trump.