Wani kamfanin gwanjon kayayyaki masu daraja a London, ya sayar da jesin mashahurin ɗanwasan Brazil, marigayi Pelé, wadda ya saka a wasan ƙarshe na Gasar Kofin Duniya na 1958.
Ranar Alhamis 16 ga Yulin 2026 ne kamfanin Sotheby ya yi gwanjon rigar da aka saya kan dalar Amurka miliyan $4.88.
Wannan adadi shi ne mafi tsadar kayan tarihi na ɗanwasan wanda ya rasu a 2022. A baya, mafi tsadar kayan Pele da aka sayar ya kai $1.33m, kan wani katin tarihin wasa na Alifabologet, a shekarar da ya rasu.
Pele ya saka jesin tun yana shekara 17, lokacin da ya zama ɗanwasa mafi yarinta da ya buga wasa kuma ya ci ƙwallo a wasan ƙarshe na kofin duniya, tarihin da har yau ba a goge shi ba.
Pele ya ci ƙwallo biyu a wasan a minti na 55 da minti na 90. Sannan bayan wasan, ya bai wa abokin wasansa, Dida, wanda ya kyautar da ita ga gidan tarihi na Museu dos Esportes a babban birnin Brazil, Rio de Janeiro.
A 2004, gidan tarihin ya miƙa jesin ga kamfanin gwanjo na Christie, don a yi gwanjon ta, inda a ƙarshe aka sayar da ita kan dala $105,600.
Pele ya saka rigar a zamanin da Brazil ta fara lashe kofin farko cikin kofin duniya biyar da take da su. Kuma rigar ta zama jesin ƙwallo ta biyu mafi tsada a tarihi, bayan ta Diego Maradona ta Kofin Duniya na 1986, wadda aka sayar kan dala miliyan $9.28.















