Adadin waɗanda suka mutu daga hatsarin bas ɗin ‘yanmakaranta a Uganda ya ƙaru zuwa yara 23 da wani balagagge ɗaya, kuma an soke dukkan tafiye-tafiye na makaranta, kamar yadda ‘yansanda suka bayyana a daren Jumma’a.
Ƙasar ta gabashin Afirka tana yawan samun haɗɗura na bas da manyan motoci a kan manyan hanyoyi.
Bas ɗin tana kan hanayrta ta dawowa babban birnin ƙasar, Kampala, daga wata tafiya ta makarantar zuwa wajen faɗuwar ruwa na Sipi Falls a gabashin Uganda ranar Alhamis ne a lokacin da motar ta kauce daga kan hanya, inda ta kashe ɗalibai 20 da wani balagagge.
Tun wancan lokacin “ƙarin ɗalibai uku sun mutu sakamakon raunukan da suka ji a hatsarin yayin da suke karɓar magani a asibiti", in ji ‘yansanda.
Kawo yanzu ba gane shida daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu ba.
Direba ya kauce wa hanya
Direban, wanda ake tunaniin ya ji munanan raunuka, rahotannui sun ce ya kauce a kan hanya ne, kuma ya daki wani babban dutse kana motar ta kife, in ji ‘yansanda.
Ranar Jumma’a, ma’aikatar ilimin ƙasar ta kira wani zama na gaggawa kuma ta yi shelar dakatar da dukkan tafiye-tafiye na makaranti a faɗin ƙasar .
Katse tafiye-tafiyen ya zo ne domin ba da damar "cikakken bincike cikin yanayin da ya haddasa haɗɗuran kwanannan nan da ke da alaƙa da ‘yan makaranta,” da inganta matakan tsaro da kuma ba da horaswa na tsaro ga makaranti da kamfanonin sufuri, in ji ‘yansanda.
Ana kan bincike
Bala’in ya auku ne kusa da Kaserem, fiye da kilomita 250 (mil 150 ) daga Kamapala, tsakanin Kapchorwa, inda wajen faɗuwar ruwa na Sipi Falls ya ke, da kuma birnin Mbale.
‘Yansanda sun fitar da wani hoto da wata bas da ta magale kum ata kife tare da bayyana cewa an fara gudanar da bincike.
Ashirin da uku daga cikin wdnada suka ji rauni suna asibiti kawo yanzu.
Saura motoci uku da suke cikin tafiyar ‘yan makarantar King David Junior School a Kampala sun koma lafiya, in ji ‘yansanda.
Akan samu haɗuran motoci a Uganda. A watan Oktoba, motocin bas biyu sun yi karo a kan wata babbar hanya, inda suka kashe aƙalla mutum 46.
Wani rahoto na shekarar 2024 ya ce an samu taho-mu-gaman motoci 4,434 da mace-mace 5,144 a cikin shekarar.




















