| Hausa
DUNIYA
3 minti karatu
An samu rahotannin cin zarafin mata kusan 9,800 a shekarar 2025, fiye da ninki biyu kan na 2024: MDD
A ranar Labara ne wakiliyar MDD ta musamman kan cin zarafin mata a lokacin rikice-rikice ta ce, an samu rahotannin cin zarafin mata da suka ninka sau biyu a duniya a shekarar 2025 fiye da bara.
An samu rahotannin cin zarafin mata kusan 9,800 a shekarar 2025, fiye da ninki biyu kan na 2024: MDD
Wakiliyar MDD ta yi nuni da cewa kusan rahotanni cin zarafi 3,000 ne aka aikata a kan yara, “wanda ke nuna karuwar kashi 37% daga bara. / Reuters

Wakiliyar Majalisar Ɗinkin Duniya ta musamman kan cin zarafin mata a lokutan rikice-rikice a faɗin duniya ta faɗa a ranar Laraba cewa, an samu sahihan rahotannin cin zarafin mata kusan dubu 10 a shekarar 2025, tana mai ƙari da cewa "adadin na iya wuce hakan ."

"Rahoton shekara-shekara na Sakatare Janar na Majalisar da aka tattaro kuma aka tabbatar da shi kan cin zarafin mata a rikice-rikice a duniya a shekarar 2025 ya kai 9,788- fiye da ninki biyu na adadin da aka samu a bara, Pramila Patten ta shaida wa zauren Majalisar Tsaro na MDD a muhawarar da aka yi kan batun, cewa: "Adadin ya fi haka, inda masu ba da agajin jinƙai a fagen suka ƙiyasta cewa, a kowanne rahoto da ya isa zuwa asibiti, ana samun 10 zuwa 20 da ba a magana ko ba da rahoto a kai.’’

Ta yi gargaɗin cewa alƙaluman na iya rage yawan matsalar saboda ‘‘samun damar zuwa wurin da abun ya faru da rashin tsaro da rushewar tsarin kulawa da rage yawan ayyukan MDD da kuma gudun ƙyama da nuna wariya da suka yi yawa a tsakanin al’umma."

Patten ta ce rahoton ya ƙunshi yanayi na damuwa 21, inda aka samu mafi yawan rahotannin cin zarafi da MDD ta tabbatar da su a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC), Haiti, Sudan, da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Yara na daga cikin waɗanda abin ya fi shafa

Ta bayyana cewa an aikata laifukan cin zarafi kusan 3,000 a kan yara, "adadin da ke wakiltar ƙarin kashi 37 idan aka kwatanta da bara."

Daga ciki an gano rahotanni 77, inda 62 daga cikinsu aka danganta da cin zarafin sakamakon rikice-rikice, sai kuma kashi 65 da masu aikata laifuka a-kai-a-kai.

Sabbin ƙarin sun haɗa da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai a DRC da Haiti, da kuma waɗanda aka samu daga Isra'ila da Rasha.

A ɓangaren Isra'ila, Patten ta ce "an yi ta samun wasu nau’ukan laifukan fyaɗe da sauran ayyukan cin zarafin mata, musamman a wuraren da aka tsare mutane, da wuraren bincike da kuma lokacin ayyukan soji, inda aka samu rahotanni masu yawa da aka tabbatar da su, duk da cewa ana matsa wa waɗanda abin ya shafa lamba kada su ba da rahoton cin zarafi."

Ɗaukar nauyi

Patten ta yi kira ga gwamanatoci da su ƙara matakan ɗaukar nauyi. Kana ta yaba wa Firaiministan DRC Judith Suminwa Tuluka a matsayin "mace ta farko da ta riƙe wannan babban mukami," inda ake sa ran DRC za ta jagoranci taron Kwamitin Tsaro na watan Yuli.

Tuluka ta jaddada cewa rahoton "ya nuna yanda ake samun ƙaruwar rahotannin cin zarafi da aka tabbatar da sahihancinsu, kuma hakan ya samar mana da tushe da hukumar da muke buƙata don muhawararmu a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo."

"Kalubalen da ke gaban mu yanzu shine tabbatar da cewa wannan matakin ya isa ga waɗanda suka tsira yadda ya kamata," in ji ta.

Da take magana kan batun rage kasafin kuɗi na gudanar da ayyukan na MDD, Tuluka ta yi gargaɗin cewa matakin ‘‘yana da tasiri sosai na kai tsaye ga rayuwar waɗanda suka tsira, da ikon da kasashe suke da shi wajen gurfanar da waɗanda suka aikata laifi, da kuma sahihancin alƙawarinmu na haɗin gwiwa, kazalika suna raunana ƙarfinmu na haɗin gwiwa don cike gibin samun rahotanni," in ji ta.