| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
4 minti karatu
Iran ta ƙaddamar da hare-hare kan sansanonin Amurka, ta yi gargaɗin faɗaɗa hare-hare
Tehran na gargadin cewa za ta fara "cikakken ayyukan kai samame" idan hare-haren Amurka a kanta suka ci gaba na tsawon kwanaki biyu ko uku.
Iran ta ƙaddamar da hare-hare kan sansanonin Amurka, ta yi gargaɗin faɗaɗa hare-hare
Kuwait ta ce wani harin Iran ya sami ɗaya daga coikin tashoshin lantarki da na tsaftace ruwan ƙasar

Taɓarbarewar lammura a Gabas Ta Tsakiya sun ci gaba zuwa dare na bakwai inda Iran ta ba da rahoton mace-mace uku daga hare-haren Amurka da kuma ƙaddamar da hare-hare kan sansanonin sojin Amurka a Kuwait da Bahrain da kuma Jordan.

Rundununar kare Juyin Juya Halin Iran ta bayyana daga farkon ranar Asabar cewa tankokin mai biyu da “hukumomin leƙen asirin Amurka mayaudara" suke ba su umarni sun tarwatse bayan sun ci karo da nakiyoyi a mashigar Hormuz, lamarin da rundunar sojin Amurka ta musanta cikin sauri.

Rundnunar Kare Juyin Juya hali ta bayyana a kafar talabijin ta ƙasar cewa ta “hana” jiragen ruwa huɗu da ke nemna wucewa ta muhimmiyar hanyar ruwan.

Sai dai kuma dakarun Amurka sun ba da rahoton kai hare-hare kan Iran da zummar "ci-gaba da kassara ikon sojin Iran," in ji wata sanarwar da hedikwatar tsaro ta Amurka ta fitar a shafin X.

A ɗaya daga cikin taɓarɓarewar lammura mafi girma tun da abokan gaban suka sake soma yaƙi, Iran ta zargi dakarun Amurka da kai hare-hare kan ababen more rayuwa na fararen hula, ciki har da wani filin jiragen sama da wata tashar jiragen ƙasa da kuma gadoji biyu, kuma ta ce ta kai hari kan kayayyakin Amurka a fadin yankin.

Shugaban Amurka Donald Trump dai ya yi gargaɗi a baya cewa zai kai hari kan ababen more rayuwan Iran, amma babu tabbaci daga ɓangaren Amurka ranar Jumma’a cewa dakarun Amurka sun fara yin hakan.

Gargaɗin Iran

Manjo Janar Mohsen Rezaei, wani babban mai ba da shawara na soji ga Jagoran Addinin Iran, ya ce Tehran za ta fara "cikakken ayyukan kai samame" idan hare-haren Amurka suka ci gaba a kanta na tsawon kwanaki biyu zuwa uku.

"Iran ba za ta sake taƙaita kanta ga hare-haren ramuwar gayya, martani na taɓa-ni-na-taɓa-ka ba...kuma babu wani kan iyaka na siyasa da zai tsira," a cewar Rezaei, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Iran, IRIB, ya ruwaito.

An fara yaƙin ne ranar 28 ga watan Fabrairu inda Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar da hare-hare masu kisa kan Iran, wadda ta ɗau fansa ta hanayar rufe mashigar Hormuz, wata muhiummiyar hanyar jigilar mai ta duniya.

Kamfain dilalancin labaran Iran IRNA ya ba da rahoto ranar Asabar cewa hare-haren Amurka sun kashe mutum uku da kuma raunata mutum takwas a lardin kudancin ƙasar na Hormozgan.

Rundunar sojin Iran ta ce ta kai hari kan wuraren sojin Amurka a Kuwait da Bahrain da Jordan a wani martani ga hare-haren Amurka, in ji wata sanarwa da kafar twasa labaran Iran ta ɗauka ranar Asabar.

A Kuwait, dakarun Iran sun kai hari kan wani wurin adana makamai a sansanin Al-Adiri, da gine-ginen hedikwatar da wurin adana makamai a sansanin Ali Al-Salem da kuma wasu gadoji na sadarwa.

A Jordan, an kai hari kan tankokin mai a sansanin Al-Azraq, kamar yadda kafar watsa labaran ƙasar ta bayyana a manahajar Telegram.

'Hukunta mai tsangwama'

Ma’aikatar makamashin Iran ta yi kira ga 'yan ƙasar su rage amfani da lantarki da kuma kashe esi ɗinsu a lokacin da aka fi amfani da wuta — yayin da zafi ke ƙaruwa a yankin — bayan lantarkin ƙasar ya kasance ƙarƙashin ƙarin matsi daga abin da ta ce hare-haren Amurka ne kan kayayyakin lantarki.

Rundunar sojin Iran ta yi barazana ga ababen more rayuwa a faɗin yankin idan aka kai hari kan ababen more rayuwarta, kuma a ranar Jumma’a ta ƙaddamar da hare-hare kan wurare da yawa.

A Kuwait, inda Tehran ta ce ta kai hari kan wuraren sojin Amurka, ma’aikatar lantarki ta ce wani harin Iran ya lalace wata tashar makamashi da ta tsaftace ruwa kuma ta yi kira ga masu amfani da lantarki su rage amfani lantarki.

Rundunar sojin Kuwait ta ce wasu dakaru sun ji rauni a lokacin da wasu jirage mara matuƙan Iran suka afka wa wasu sansanoni

Rundunar kare Juyin Juya halin Iran ta ce ta kai hari a kan tsarin na’urar hango nesa na Amurka a Qatar domin "hukunta mai tsangwaman", yayin Doha ta ce ta kakkaɓo wani makami mai linzami.

Rundunar ta ce ta kai hari kan wuraren na’urori hangen nesan Amurka a Oman da kuma sansanin sojin Al-Tanf a Syria. Wata majiyar sojin Syria ta musanta cewa an kai wani hari kuma dakaraun Amurka sun ce sun janye daga sansanin daga farkon wannan shekarar.

Ma’aikatar lafiyar Iran ta ce an kashe aƙalla mutum 38 kuma an raunata fiye da mutum 400 a ƙasar tun lokacin da Amurka ta fara kai hare-hare.

Masu shiga tsakani sun yi ƙoƙarin su dawo da ɓangarotin biyu kan teburin tattaunawa kuma China da Pakistan sun yi kira ga Amurka da Iran su daina yaƙi kuma su sake fara tattaunawa.

Rumbun Labarai
Trump ya ƙi goyon bayan Netanyahu don sake tsayawa takara
Kotun Kolin Isra’ila na sauraren daukaka karar hukuncin hana ‘yantakara Larabawa shiga zabe
Jirgin FlyDubai ya yi saukar gaggawa a Saudiyya bayan da matuƙan biyu suka kaure da faɗa
Ghalibaf na Iran ya yi gargaɗin cewa babu ƙasar da za ta iya sayar da mai idan aka hana Tehran
Shin Isra’ila ta yi yunkurin kawar da tunanin wanzuwar Falasɗinu baki daya?
Iran za ta tilasta wa Amurka ficewa daga Gabas ta Tsakiya: Khamenei
Sojin ruwan Amurka takwas sun jikkata a harin makami mai linzami da Iran ta harba a Mashigar Hormuz
Erdogan: Yarjejeniyar Makka ba ta da manufa a kan Iran ko Isra’ila
Ƙungiyar yarjejeniyar tsaro ta Makka ta tattauna kan yin taron gaggawa don tallafa wa Saudiyya
Abbas ya yi gargaɗin cewa manufofin Isra’ila na barazana ga wanzuwar Falasdinu
Iran ta yi tayin sake buɗe Mashigar Hormuz cikin kwanaki bakwai idan Amurka ta sassauta matsin lamba
Birtaniya za ta bai wa Saudiyya 'kariyar' soji don daƙile hare-haren 'yan Houthi
Amurka ta ce za a dakatar da zirga-zirgar dukkan kamfanonin jiragen saman Iran a duniya daga Laraba
Qatar ta ce ana ci gaba da ƙoƙarin farfaɗo da tattaunawa tsakanin Amurka da Iran
Dalilan da suka sanya Netanyahu yunƙurin hana jam’iyyun Larabawa shiga zaɓe a Isra'ila
Yaƙin Amurka da Iran ya laƙume $150B na tattalin arzikin ƙasashen Larabawa a cikin wata guda: MDD
Amurka ta hana shugaban Falasɗinawa bizar halartar Babban Taron MDD a karo na biyu
Kungiyar OIC ta yi Allah wadai da hare-haren 'yan Houthi a Makka da yankin Madina
Yaƙin Yemen ya raba fiye da mutum 100,000 da muhallansu — Majalisar Ɗinkin Duniya
Iran ta ba da umarni a yi shirin yaƙi da tsagaita wuta da yanayin bayan yaƙi ga dukkan ƙasar