Wani babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadin cewa Isra'ila ta bayar da wani umarni da ba a taba ganin irin sa ba na kwace filayen Falasdinawa don gina kayayyakin more rayuwa ba bisa ka'ida ba a wani bangare na Gabar Yamma da aka mamaye wanda aka ware wa hukumar kula da farar hula da tsaro ta Falasdinawa.
Da yake yi wa Kwamitin Tsaro jawabi a ranar Litinin, Ramiz Alakbarov, mukaddashin mai kula da harkokin zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya kan Gabas ta Tsakiya, ya ce umarnin ya shafi filayen da ke kusa da Qabatiya, kudu da Jenin, don gina hanya da ta hada Noa da Emek Dotan, biyu daga cikin matsugunan haramtacciyar kasar Isra'ila 34 da aka amince da su kwanan nan.
"Wannan shi ne karo na farko da aka rawaito kwace filayen yankin ‘Area A’ musamman don gina kayayyakin more rayuwa," in ji shi.
Kudurin Majalisar Tsaro mai lamba 2334, wanda aka amince da shi a shekarar 2016, ya ayyana matsugunan Isra'ila a yankunan Falasdinawa da aka mamaye, ciki har da Gabashin Kudus da aka mamaye, a matsayin haramtacciyar hanya kuma yana bukatar a dakatar da dukkan ayyuka a matsugunan nan take.
Da yake gabatar da rahoton babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya na 39 kan aiwatar da kudurin, Alakbarov ya yi gargadin cewa ci gaba da fadada matsugunan ba bisa ka'ida ba yana barazana ga dorewar kasar Falasdinu mai zaman kanta, mai 'yancin kai da kuma hadin gwiwa.
Alakbarov ya ce, "Samun matsugunan da ke kara fadada cikin sauri, gami da cibiyoyin tsaro, yana faruwa ne tare da karuwar hare-haren 'yan kama wuri zauna."
"Waɗannan abubuwan sun sabawa dokokin kasa da kasa, suna kara dagula mamayar haramtacciyar kasar Isra'ila da kuma lalata 'yancin al'ummar Falasdinu na neman 'yancin kai."
Mahimmancin batun Qabatiya ya wuce na titin kansa. Umarnin na daukar filaye don gina kayayyakin more rayuwa na haramtacciyar kasar Isra'ila a cikin yankin da aka bai wa gwamnatin Falasdinu a karkashin Yarjejeniya Oslo, wanda hakan ke kara lalata tushen yankin da gwamnatin Falasdinu za ta kafa da kuma kasar da za ta kafa nan gaba.
Me ya sa yankin A ke da muhimmanci
A ƙarƙashin Yarjejeniyar Oslo ta Biyu ta 1995, an raba Gabar Yamma da aka mamaye zuwa Yankuna A, B da C, tare da tsare-tsare daban-daban don ikon Falasdinawa da Isra'ila.
An sanya Yankin A a ƙarƙashin kulawar tsaron farar hula da na cikin gida na Falasdinawa. Yankin B yana da ikon kula da farar hula na Falasdinawa da tsaron Isra'ila, yayin da Yankin C, wanda ya mamaye kusan kashi 60 cikin 100 na yankin, ya ci gaba da kasancewa ƙarƙashin cikakken ikon Isra'ila.
Alakbarov ya bayyana sabon umarnin Isra'ila a matsayin farkon rahoton kwace ƙasar Yankin A musamman don kayayyakin more rayuwa. A ƙarƙashin tsarin Oslo, an keɓe Yankin A ga hukumomin kula da farar hula da na cikin gida na Falasdinawa.
Ministan Kuɗi na Isra'ila Bezalel Smotrich ya yi kira a fili da a karɓe yankin Falasdinawa kamar yadda aka umarta a ƙarƙashin yarjejeniyar.
"Koma dai mene ne, Oslo ba ta da amfani. Koma dai mene ne, Yankuna A da B su ma namu ne," in ji shi a ranar 8 ga Satumba.
Ministan Tsaron Ƙasa Itamar Ben-Gvir shi ma ya goyi bayan soke Yarjejeniyar Oslo, inda jam'iyyarsa ta Jewish Power ta gabatar da dokoki da ke neman a soke su.
Ben-Gvir ya bayyana yarjejeniyoyin a matsayin "ɗaya daga cikin manyan kura-kuran da aka yi a tarihin ƙasar", a cewar wani bincike da kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya buga, kuma ya yi kira da a sauya wannan kuskuren.
Hade matsugunai, rarraba Falasdinawa
Umarnin hanyar Qabatiya ya zo ne a daidai lokacin da ake faɗaɗa matsugunan da ba sa bisa ƙa'ida da kuma kayayyakin more rayuwa.
A cewar alkaluman da aka gabatar a cikin bayanin Alakbarov, hukumomin Isra'ila sun amince da rukunin gidaje 8,085 ba bisa ƙa'ida ba a Gabar Yamma da aka mamaye da kuma mamaye Gabashin Urushalima a lokacin rahoton, wanda ya fara daga 13 ga Yuni zuwa 18 ga Satumba.
A gefe guda kuma, hukumomin Isra'ila sun buga tayin yin gini na kusan rukunin gidaje 2,240 a Yankin C, ciki har da 1,234 a cikin hanyar "E1" kusa da Gabashin Urushalima da aka mamaye.
Alakbarov ya bayyana E1 a matsayin "barazana mai wanzuwa" ga ƙasar Falasɗinu mai dorewa kuma ya yi gargaɗin cewa ci gaba da "ƙara matsugunan" ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa.
Wurin ya bayyana ƙalubalen da ake fuskanta. E1 ta mamaye ɗaya daga cikin alaƙar ƙasa ta ƙarshe tsakanin Ramallah a arewa da Baitullahim daga kudu.
Kasar da ake ci gaba da kacalcala ta
Alakbarov ya yi gargadin cewa aikin zai yanke alaƙar da ke tsakanin arewa da kudancin Gabar Yamma da kuma ƙara ware Gabashin Urushalima daga sauran yankunan.
Smotrich ya gabatar da ginin matsugunan da ba sa bisa ƙa'ida a fili a matsayin hanyar batar da ƙasar Falasɗinu.
"Wannan gaskiyar ta ɓoye ra'ayin ƙasar Falasɗinu," in ji shi lokacin da yake sanar da shirin E1 mai cike da ce-ce-ku-ce a watan Agustan 2025.
Ya bayyana gidajen matsugunan Isra'ila ba bisa ƙa'ida ba, unguwanni da hanyoyi a matsayin tofa yawun Isra'ila a fuskar ƙasashen da ke neman amincewa da Falasɗinu.
Masana sun yi gargaɗin cewa yayin da matsugunan Isra'ila ba bisa ƙa'ida ba ke ƙara haɗuwa, ƙasar da ake da ita mallakin ƙasar Falasɗinawa za ta ƙara wargajewa.
Kauyuka sun zama kufai yayin da matsugunan ‘yan kama wuri zauna ke karuwa
Alakbarov ya kuma danganta faɗaɗa matsugunan da hare-haren da mazauna ba bisa ƙa'ida ba suka kai da kuma korar al'ummomin Falasɗinawa daga gidajensu.
Tashin hankalin da ya ci gaba da barkewa a ƙauyuka uku na Falasɗinawa, wanda ya kawo adadin al'ummomin karkara da suka rasa matsugunansu zuwa 49 tun daga watan Janairun 2023, a cewar alkaluman da aka gabatar a cikin bayanin.
Hukumomin Isra'ila sun kuma rushe ko kwace kadarorin Falasɗinawa 536 a Gabar Yamma da aka mamaye, ciki har da Gabashin Kudus da shi ma aka mamaye, inda suka kori mutane 736, cikin su har da yara 347, a cewar alkaluman.
Alakbarov ya ce kusan ba zai taba yiwuwa Falasdinwa su samu izinin gini daga mahukuntan Isra'ila ba.
A halin yanzu, sama da Falasɗinawa 33,000 mazauna sansanonin 'yan gudun hijira na Jenin, Tulkarem da Nur Shams na ci gaba da ƙaura bayan harin da sojojin Isra'ila suka kai.
"Ina matukar damuwa da yawan korar Falasɗinawa a Gabar Yamma, inda aka raba al'ummomi gaba ɗaya, wasu lokuta da dama, wanda hakan na iya haifar da damuwa game da tsarkake ƙabila," in ji Alakbarov.
‘Ba za a iya kawar da Falasɗinu ko yin biris da kasar ba’
Wakilin Falasdinu a Majalisar Dinkin Duniya Riyad Mansour ya shaida wa majalisar cewa mamaye Falasdinu ba bisa ka'ida ba ya riga ya fara faruwa ta hanyar kwace filaye da faɗaɗa matsugunan da ba sa bisa ka'ida.
Ya yi gargaɗin cewa tayin yin gine-gine a "hanyar E1" wani ɓangare ne na ƙoƙarin lalata yiwuwar kasancewar ƙasar Falasdinu, yayin da matakan raunana Hukumar Falasdinu ke iya haifar da ƙarin gudun hijira.
Mansour ya yi kira ga gwamnatoci da su hukunta waɗanda ke ci gaba da mamaye ƙasar, ci har da ta hanyar hulɗar kuɗi da kasuwanci.
"Lokaci ya yi da za a matsa daga kalamai zuwa daukar matakai, daga yin Allah wadai zuwa sauke nauyi, da kuma daga fitar da sanarwar goyon baya zuwa aiwatarwa," in ji shi.
Duk da faɗaɗa matsugunan da ba sa bisa ka'ida, Mansour ya dage cewa goyon bayan ƙasashen duniya ya nuna cewa ba za a iya gogewa ko yin watsi da Falasdinu ba, kuma ba za a iya kawar da haƙƙin Falasdinu ta hanyar mamayar Isra'ila ko mamaye su ba bisa ka'ida ba.





















