A ranar Jumma'ar nan China ta fadada janye haraji ga dukkan ƙasashen Afirka da ke da alaƙar diflomasiyya da ita, matakin na nufin ƙarfafa dangantakar kasuwanci da tallafa wa cigaban masana'antu a faɗin nahiyar, in ji kafofin watsa labarai na gwamanati.
A karkashin sabuwar manufar, an cire harajin shigo da kaya daga ƙasashen Afirka 53, ciki har da ƙasashe masu tasowa kamar Kenya, Masar, da Nijeriya, in ji kamfanin dillancin labarai na Xinhua.
Shirin ya dora ne a kan matakan da suka gabata waɗanda suka ba da cikakken keɓe haraji ga ƙasashe 33 mafi ƙarancin ci gaba na nahiyar.
Jigilar kaya ta farko da ta amfana daga faɗaɗa manufar -- tan 24 na tuffa daga Afirka ta Kudu -- ya samu amincear jami’an fito a Shenzhen ranar Juma'a, wanda hakan ke nuna alamar fara samun damar shiga kasuwa ga kayayyakin Afirka.
Hukumomin kasuwanci na China sun ce matakin zai bai wa fitar da kaya daga Afirka -- daga coacoa da coffee zuwa 'ya'yan itatuwa da ‘ya’yan inabi -- wani matsayi mai kyau a kasuwar China, inda irin waɗannan kayayyaki a baya ke fuskantar harajin da ya kama daga kashi 8 zuwa 30.
Jami'ai kuma na sa ran cewa manufar za ta ƙarfafa saka hannun jari a masana'antun sarrafa kayayyaki na Afirka, wanda ke taimakawa wajen sauya tattalin arziki fiye da fitar da kayan masarufi.
China ta kasance babbar abokiyar kasuwancin Afirka, yayin da kasuwanci tsakanin China da Afirka ya kai matsayi mafi girma na dala biliyan 348 a shekarar 2025. Daga cikin wannan jimillar, kayayyakin da China ke shigara daga Afirka sun kai dala biliyan 123, karuwar kashi 5.4 a shekara.
Sabon matakin na janye harajin ya yi daidai da babban ƙoƙarin da China ke yi na zurfafa bude kofofin tattalin arziki.
A ƙarƙashin Tsarin Shekaru Biyar karo na 15 na China, Beijing na da niyyar ƙara buɗe kasuwanninta yayin da take gina yanayi na gaskiya, kwanciyar hankali, da kuma hasashen kasuwanci.
Hukumomi sun kuma yi alƙawarin haɓaka inganci da faɗaɗa haɗin gwiwar cinikayya da saka hannun jari har zuwa shekarar 2030.












