| Hausa
NIJERIYA
3 minti karatu
Dakaru sun kassara 'yanta'adda da ceto waɗanda aka yi garkuwa da su a samame a Sokoto da Katsina
Rundunar tsaro ta musamman (ta arewa maso yammacin Nijeriya), ta ce ta kai jerin samamen ne tsakanin ranakun 21 zuwa 22 na watan Yuni a wani ɓangare na ƙoƙarin yaƙar ta’addanci da fashin daji a yankin.
Dakaru sun kassara 'yanta'adda da ceto waɗanda aka yi garkuwa da su a samame a Sokoto da Katsina
TSOHON HOTO: Sojojin Nijeriya na fita wajen yaƙar 'yanbindiga masu aikata ta'addanci / Reuters

Dakarun rundunar Operation Fansan Yamma sun cim ma muhimmiyar nasara a ayyukan da suke yi na yaƙar ta’addanci a faɗin jihohin Sokoto da Katsina, inda suka kassara wasu ‘yanta’adda tare da ceto waɗanda aka yi garkuwa da su da kuma ƙwato makamai da dabbobi da sauran kayayyaki da ƙungiyoyin masu aikata laifukan ke amfani da su.

Rundunar tsaro ta musamma (ta arewa maso yammacin Nijeriya), ta ce ta kai jerin samamen ne tsakanin ranakun 21 zuwa 22 na watan Yuni a wani ɓangare na ƙoƙarin yaƙar ta’addanci da fashin daji a yankin.

A jihar Sokoto, dakaru sun mayar da martani cikin gaggawa kan wasu rahotannin sirri da ke nuna cewa ‘yanta’adda da makamai na ƙoƙarin kutsa garin Tureta ranar 21 ga watan Yuni.

Dakarun tsaro sun yi arangama da maharan, inda suka tilasta musu barin abin da ya kawo su kuma suka tsere daga wurin.

Bayanan sirri da aka tattara ta sama sun gano ‘yantaddan da ke tserewa zuwa ta ƙauyen Sulubawa Gidan Kare, inda rahotanni suka ce suna tafiya da fararen-hula da aka yi garkuwa da su da kuma dabbobi.

Dakaru sun ƙaddamar da samame na bin su kuma sun gamu da turjiya daga ‘yanta’addan, waɗanda suka yi kwanton ɓauna yayin da suke ja da baya.

Duk da harin, dakaru sun fi ƙarfin masu aikata laifukan, inda suka tilasta su su tarwatse.

Samamen ya yi sanadiyyar nasarar ceto waɗanda aka yi garkuwa da su da ƙwato dabbobin da aka sace da kuma babura biyu da aka yi zargin cewa ‘yanta’addan na amfani da su.

A wani aikin na daban da aka yi a sanyin safiyar ranar 22 a watan Yuni, dakaru sun ƙaddamar da wani samame bisa bayanan sirri a kan wata maɓoyar ‘yanta’adda a ƙaramar hukumar Matazu ta jihar Katsina.

Harin na sanyin safiya ya shammaci ‘yanta’addan, lamarin da ya haddasa zazzafar musayar wuta. An kashe mutum biyu da ake zargi da kasancewa ‘yanta’adda ne, yayin da saura suka tsere da raunin bindiga.

Dakarun tsaro sun ƙwato tarin makamai da kayayyaki daga maɓoyarsu, ciki har da bindigogi da wasu makaman da babura uku da kayayyakin sadarwa da kuma dabbobin da aka sace.

Hukumomin tsaro sun bayyana samamen a matsayin wata manuniya ta jajircewa da kuma ƙwarewa ta dakarun da aka tura a ƙarƙashin dakarun Operation Fansan Yamma.

"Nasarorin kwannan nan sun nuna jajircewa babu ƙaƙƙautawa da ƙwarewa da kuma juriya ta dakaru wajen kai yaƙi kai-tsaye ga wuraren ‘yanta’adda da masu aikata laifuka," kamar yadda rundunar ta musamman ta bayyana a wata sanarwa.

Runundar sojin ta sake bayyana jajircewarta ga ɗorewar ayyukan samame da zummar tarwatsa ƙungiyar da hana ƙungiyoyin masu aikata laifuka ‘yancin kai komo da kuma dawo da zaman lafiya da tsaro a faɗin yankin arewa maso yammacin Nijeriya.