Kotu a Birtaniya ta wanke tsohuwar Ministar Man Fetur ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke, daga dukkan zargin cin hanci da rashawa da ake tuhumarta da su, bayan kwashe tsawon lokaci ana gudanar da shari'ar.
Hukuncin na Kotun Southwark Crown Court ya biyo bayan shafe shakaru tsohuwar ministar tana fuskantar tuhumar cin hanci da rashawa a Birtaniya da Nijeriya.
Kwamitin alƙalan ya yanke hukuncin cewa tsohuwar ministar ba ta da laifi a kan dukkan zargi guda shida na karɓar na-goro da kyautuka na alfarma da aka gabatar a kanta.
Hukumar Yaƙi da Manyan Laifuka ta Burtaniya (NCA) ce ta shigar da ƙarar, inda ta zargi Alison-Madueke da karɓar kyaututtuka na miliyoyin fama-famai domin ba da kwangilolin mai na biliyoyin daloli lokacin da take minista.
Waɗannan alfarma sun haɗa da hayar jiragen sama, da gidaje na alfarma a Landan, da sauran hidimomin rayuwa ta kece raini tsakanin shekarun 2011 zuwa 2015.
Bayan ga tsohuwar ministar, kotun ta kuma wanke wasu mutane biyu da ake tuhuma tare da ita. Mutanen sun haɗa da ɗan uwanta, Doye Agama, da kuma wata jami'ar harkar mai, mai suna Olatimbo Ayinde, waɗanda aka zarga da taimaka mata wajen karɓar ko ɓoye waɗannan abubuwan more rayuwa.
Hukuncin na kotun Landan ya kawo ƙarshen bincike mai sarkakiya da aka kwashe shekaru 11 ana gudanarwa a kan tsohuwar ministar. Hukumar NCA ta ƙasar Burtaniya ta fara bincikar lamarin ne tun a shekarar 2015, jim kaɗan bayan da ta bar ofis sakamakon saukar gwamnatin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan daga mulki.
A lokacin da ake tsaka da shari'ar, lauyoyin Diezani sun jaddada cewa babu wata shaida da ke nuna cewa ta karya doka ko ta karɓi rashawa domin fifita wasu kamfanonin mai. Ita ma kanta tsohuwar ministar ta sha musanta waɗannan zarge-zarge, inda ta bayyana cewa dukiyarta da kadarorinta ta same su ne ta halastacciyar harnya, kuma babu laifi a cikinsu.
Labarin wanke Diezani ya sake tayar da muhawara mai zafi a tsakanin masu fashin baki kan sha'anin siyasa da shari'a a Najeriya.
Kafin wannan lokaci, hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa na Najeriya sun sha ƙoƙarin ganin an mayar da ita gida domin fuskantar shari'a, sai dai hakan bai yiwu ba sakamakon rashin lafiyar da ta ce tana fama da ita da kuma shari'ar da take fuskanta a Birtaniya.
Diezani Alison-Madueke, wadda ita ce mace ta farko da ta taɓa riƙe mukamin Ministar Man Fetur a Najeriya sannan kuma mace ta farko da ta jagoranci ƙungiyar ƙasashe masu arzikin mai ta duniya (OPEC), ta kasance ɗaya daga cikin manyan mutanen da aka fi tattaunawa a kansu dangane da yaƙi da cin hanci da rashawa na ƙasa da ƙasa a cikin shekaru goman da suka gabata.















