| Hausa
NIJERIYA
5 minti karatu
Shugaba Tinubu ya amince a ɗauki jami'an kare daji 1,000 a Jihar Katsina
Lamarin na zuwa ne yayin da jihar Katsina da ke arewa maso yamacin ƙasar ke ci gaba da fama da fashin daji da garkuwa da mutane da sace shanu.
Shugaba Tinubu ya amince a ɗauki jami'an kare daji 1,000 a Jihar Katsina
Gwamnan Jihar Katsina Umaru Dikko Radda ne ya bayyana hakan. / Dikko Radda Facebook

Shugaba Bola Tinubu ya amince a ɗauki jami’an kare daji 1,000 a jihar Katsina, a wani mataki na ƙarfafa ayyukan tsaro a garuruwan da ke daji da kuma wuraren da ‘yanbindiga ka iya kai hare-hare.

Gwamnan jihar Dikko Radda ne ya bayyana amincewar ranar Talata yayin da yake jawabi ga manema labarai bayan ya gana da malamai da sauran masu ruwa da tsaki kan ƙoƙarin yaƙar rashin tsaro a jihar, kamar yadda jaridar Premium Times ta wallafa.

Lamarin ya zo ne yayin da jihar da ke arewa maso yammacin Nijeriya ke fama da fashin daji da garkuwa da mutane da satan shanu a faɗin ƙananan hukumomin da ke cikinta, musamman wuraren da ke kusa da dazuka da suka daɗe da kasancewa wuraren ɓuya ga ƙungiyoyin ‘yanbindiga.

“Ina so na nuna godiyata ga shugaban ƙasa da amincewa da ya yi ga buƙatarmu ta ɗaukar matasa masu jini a jika 1,000 maza da mata a matsayin masu kare daji.

“Za su yi aiki tare da hukumomin tsaro na yau da kullum da jami’an tsaron kiyaye al’ummomi ,” kamar yadda Radda ya bayyana.

Gwamnan ya ce za a bai wa waɗanda za a ɗaukar horo na musamman tare da ba su kayayyakin aiki domin taimaka wajen ayyukan tsaro a wurare masu nisa da wurare masu dazuka inda ƙungiyoyin masu laifi ke aika-aika.

Ya kuma yaba wa gwamnatin tarayya game da abin da ya kira tura ƙarin sojoji da ‘yansanda da jami’an tsaro na farin kaya zuwa jihar.

“Yawan jami’an soji da ‘yansanda da jami’an tsaro na farin kaya da aka tura abu ne mai ƙara ƙwarin gwiwa. Wannan wani haɗaɗɗen mataki ne da muka ji daɗinsa sosai,” in ji shi.

Dabarar tsaro bisa al’ummomi

Amincewar ta ƙara nuna yadda jihar Katsina ke daɗa dogaro ga tsare-tsaren tsaro da suka dogara kan al’umma yayin da hukumomi ke neman tallafa wa ayyukan soji kan ƙungiyoyin ‘yanbindiga da ke aika-aika a arewa maso yammacin ƙasar.

Tuni dai rundunar tsaron al’umma da jihar ta kafa ta fara aiki domin taimaka wa ayyukan hukumomin tsaro wajen samar da bayanai na tsaro.

Radda ya ce zaman lafiya mai ɗorewa zai buƙaci haɗin kai tsakanin hukumomin tsaro da al’ummomin jihar , yana mai cewa mazauna sukan kasance da muhimman bayanai da ke da ƙarfin iya tarwatsa ƙungiyoyin masu aikata laifuka.

Ya ƙara da cewa tattaunawa da shugabannin addini wani ɓangare ne na samar da martani na al’ummomi ga rashin tsaro.

“Manufar wannan ganawar ita ce na ji kai tsaye daga malaman addinin Musulunci, na fahimci ra’ayoyinsu game da matsalar tsaron da muke fuskanta a yanzu da kuma neman shawarwarinsu game da yadda ya kamata a bi da shi,” in ji shi.

Gwamnan ya ce yaƙar rashin tsaro na buƙatar ƙarin matakai na soji.

“Yaƙi da fashin daji ba abu ne da za a iya bari wa hukumomin tsaro kawai ba. Gudunmawar la’ummomi na da muhimmanci wajen samun zaman lafiya mai ɗorewa,” kamar yadda ya bayyana .

Ƙungiyoyin masu aikata laifuka suna da mutane cikin al’ummomi

Radda ya ce bincike da nazarin tsaro sun nuna cewa ƙungiyoyin masu aikata laifuka suna dogara ne da masu taimaka musu a cikin al’ummomi.

Ya ce wasu daga cikin mazauna wuraren ne ke taimaka wajen kai kayayyaki da bayanai da ga ƙungiyoyin ‘yan bindiga tare da taimaka wajen sayar da dabbobin da suka sace.

“Yawancin yadda suke samun kayayyaki da bayanai da ma sayar da dabbobin da suka sace na da alaƙa ne da mutane da ke zaune cikinmu. Wannan shi ne ya sa akwai buƙata ta wayar da kan dukkan al’ummomi saboda kowa ya ba da nasa gudumowar,” in ji shi.

Ya bayyana malaman addinin Musulunci a matsayin muhimman abokan aiki wajen tallata ɗabi’u na zamantakewa na gari da kuma hana mutane ɗabi’u da ke taimaka wa aikata laifuka .

“Malamai suna taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar ɗabi’u na gari na al’umma . Mun gabatar da ƙalubalen gare su kuma mun nemi shawarwarinsu yayin da muke aiki domin samun mafita mai ɗorewa,” in ji shi .

Ƙayyade amfani da babura da siyar da man fetur

Gwamnan ya kuma bayyana cewar jihar za ta ci gaba da aiwatar da matakai na katse ikon aika-aikar ƙungiyoyin ‘yanbindiga.

Ya yi ishara ga wani matakin ƙayyade kaikomon babura a wasu ƙananan hukumomin da ke kusa da matsalar, ciki har da Musawa da Matazu, inda dakarun tsaro suka zafafa ayyukansu kan ɓarayin daji.

“Mun ɗauki muhimman matakai, ciki har da hana amfani da babura a wasu ƙananan hukumomin da lamarin ya shafa irin su Musawa da Matazu, tare da ƙayyade amfani da na’urar POS da kuma wuraren cajin waya da ke taimaka wa aikata laifuka,” in ji shi.

Radda ya kuma yi magana game da matakin da jihar ta ɗauka kwanan nan na ƙayyade sayarwa da kuma safarar mai a cikin jarkoki, wani mataki da hukumomi suka ce an yi shi ne domin yanke hanyar samun kayayyaki ga ƙungiyoyi ‘yanbindiga da ke aika-aika a cikin dazuka.

An bayyana matakin ne ranar Litinin bayan wani zaman tsaro na gaggawa tare da hukumomin tsaro da sarakunan gargajiya.

Gwmanan ya ce, an ɗauki matakan ne bayan an tattauna da shugabannin al’ummomin da lamarin ya shafa.

“An bayyana waɗannan matakan bayan tattaunawa da shugabannin al’ummomi daga wuraren da lamarin ya shafa, kuma za mu ci gaba da tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaki domin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali,” in ji shi.