Majalisar Wakilan Nijeriya ta amince da wani kudiri a ranar Alhamis, wanda ya share fage ga jihohi 36 ciki har da babban birnin kasar su kafa rundunar 'yan sandansu, wani mataki da aka daɗe ana muhawara a kai da nufin magance matsalar rashin tsaro a Nijeriya.
Wannan mataki zai taimaka wajen ƙara kusancin tsarin ‘yansanda da yanayin abubuwan da ke faruwa a yankunansu, yayin da hukumomi ke neman hanyoyin magance matsalolin tsaro daban-daban da suka mamaye tsarin da kuma iko da ake samu daga sama.
Magoya bayan tsarin, ciki har da Shugaba Bola Tinubu, suna ganin raba iko tsakanin gwamnatin tarraya da na jihohi a bangaren ‘yansanda yana da matukar muhimmaci wajen daukar matakai ga matsalolin tsaro da suka hada da tayar da zaune tsaye da sace-sacen jama’a don ƙarban kuɗin fansa da kuma rikicin kabilance da sauransu waɗanda suka bazu a yawancin sassan Nijeriya.
Mafi yawan 'yan majalisar wakilan Nijeriya sun kada kuri'a kan ƙudirin kundin tsarin mulki yayin da ake sa ran Majalisar Dattawa za ta amince da shi kuma ta zartar daga baya a ranar Alhamis.
Wannan gagarumin mataki ne da zai bai wa gwamnatocin jihohi 36 na Nijeriya damar kafawa da kuma kula da rundunar 'yansandansu tare da sauran waɗanda ake da su na tarayya.
Dokar, wadda ta samu goyon baya daga ‘yan jam'iyyu daban-daban, kazalika dole ne ta samu amincewa daga akalla kashi biyu bisa uku na dukkan majalisun jihohi kafin ta fara aiki.
A lokuta da dama gwamnonin jihohi sun sha bayyana cewa ana dora musu alhakin tsaro amma a zahiri ba su da ikon yin kataɓus ko nuna iko da ‘yansanda a jihohinsu.
Haka kuma masu fafutukar kawo sauyi sun bayyana cewa 'yansandan jihohi za su iya taimaka wajen inganta lokutan mayar da martani, ƙarfafa tattara bayanan sirri da kuma tura jami'ai waɗanda suka fi sanin al'ummomin yankin.
Yayin da masu sukar mataki ke gargaɗin cewa, gwamnoni za su iya amfani da 'yan sandan jihohi ta hanyar da bata dace ba kan abokan hamayya ko tsiraru.
Kazalika akwai tambayoyi kan kuɗaɗen tallafi, da matakan horo da kuma haɗin gwiwa a tsakani, inda masu sharhi suka ce jihohi marasa karfi na iya fuskantar tsaiko wajen gudanar da ayyukan ‘yansandan.


.jpeg?width=720&format=webp&quality=80)


.jpeg?width=128&format=webp&quality=80)










