Dembele, Guler, Mbappe, Messi, Ronaldo: Shahararrun ’Yanwasa 15 da za su haskaka Gasar Kofin Duniya
WASANNI
18 minti karatu
Dembele, Guler, Mbappe, Messi, Ronaldo: Shahararrun ’Yanwasa 15 da za su haskaka Gasar Kofin DuniyaGasar, wadda za ta kunshi kasashe 48 da wasanni 104 da za a fafata a kasashen Amurka, Canada, da Mexico, za ta hada manyan taurarin duniya, matasa masu tasowa, da tsofaffin ’yanwasa da ke neman daukaka ta karshe kafin su yi ritaya.
Fiye da 'yan wasa 1,200 ne za su taka leda a gasar cin kofin duniya, amma kalilan ne kawai za su bar sunayensu a rubuce a tarihin kwallon kafa. / TRT World

Yayin da gasar cin kofin duniya ta kasance babban mataki mafi girma a harkar kwallon kafa, gasar ta shekarar 2026 an tsara ta ne domin ta zama mafi girma a tarihi.

Gasar, wadda za ta kunshi kasashe 48 da wasanni 104 da za a fafata a kasashen Amurka, Canada, da Mexico, za ta hada manyan taurarin duniya, matasa masu tasowa, da tsofaffin ’yanwasa da ke neman daukaka ta karshe kafin su yi ritaya.

Duk da cewa fiye da ’yanwasa 1,200 ne za su fafata, kalilan ne kawai daga cikinsu za su rubuta sunayensu a tarihin kwallon kafa.

Sakamakon matsin lamba mai yawa da kuma yadda kowane dakika ke da muhimmanci, zura kwallo guda daya, tare kwallo da mai tsaron raga zai yi, ko kuma wani lokaci na bajinta na iya sauya daukakar dan wasa har abada.

Tashar TRT World ta kawo bayani daki-daki kan manyan ’yanwasa 15 da ake kyautata zaton za su taka rawar gani a kungiyoyinsu yayin gasar, sannan su faranta wa masoya kwallon kafa rai da wasanni da za a dade ba a manta su ba.

Lamine Yamal (Spain)

Yana da sauki mutum ya manta cewa Yamal yana da shekaru 18 kacal, idan aka yi la’akari da manyan nasarorin da ya samu da kungiyar Barcelona da kuma kasar Spain.

Dan wasan gaba na Barcelona ya taimaka aka zura kwallaye 27 a gasar La Liga a kakar wasa ta 2025-26, inda ya zura kwallaye 16 sannan ya taimaka aka zura guda 11. Bugu da kari, ya zura kwallaye shida kuma ya taimaka aka zura hudu a gasar zakarun Turai ta UEFA Champions League.

Ya taka rawar gani sosai wajen jagorantar Spain domin lashe Kofin nahiyar Turai na UEFA Euro 2024, inda ya zama dan wasa mafi karancin shekaru da ya taba buga wasa kuma ya zura kwallo a gasar, sannan ya karkare gasar a matsayin wanda ya fi kowa taimakawa aka zura kwallaye da kwallaye guda hudu.

A kakar wasan da ta wuce, ya rika samun maki kusan 8.0 cikin 10 a kowane wasa.

A halin yanzu, Yamal ba ya buga wasa saboda raunin da ya samu a wata jijiyarsa ta bayan cinya lokacin da Barcelona ta doke Celta Vigo a gasar La Liga a watan Afrilu, lamarin da ya janyo fargabar cewa wata kila ba zai buga wasan farko na rukuninsu da kasar Spain za ta buga ba.

Sai dai, babban kocin kungiyar, Luis de la Fuente, ya tabbatar da cewa Yamal yana kan hanyar murmurewa domin buga wasan farko na Spain a gasar cin kofin duniya da za su fafata da Cape Verde a mako mai zuwa.

Kylian Mbappe (France)

Ana kallon Mbappe a matsayin daya daga cikin ’yanwasan da suka fi kwarewa a kowane fanni a duniyar kwallon kafa, inda masana da yawa ke daukarsa a matsayin wanda ya fi kowa fice a duniya baki daya.

Shi gwanin zura kwallaye kamar haka aka hallice shi, yana da gudun gaske, da kuma dabarun doke masu tsaron baya a fafatawar gaba da gaba.

Yana da shekaru 19, ya jagoranci Faransa wajen lashe kofin duniya na 2018. A shekarar 2022 kuma, ya sake kai kungiyarsa zuwa wasan karshe da suka fafata da Argentina.

Dan wasan na Faransa mai shekaru 27 zai nemi ya sake kafa wani babban tarihi a gasar kofin duniya ta 2026 bayan bacin rai mafi girma da ya fuskanta a Qatar, duk da cewa ya zura kwallaye uku rigis a wasan karshe na 2022.

A wata hira ta nishadi ta amsa tambayoyi cikin gaggawa da ya yi kwanan nan da mai shirya bidiyoyin intanet Finn Agostinelli, an bukaci Mbappe da ya yi hasashen wanda zai fi zura kwallaye a gasar cin kofin duniya ta 2026 tsakanin fitattun ’yanwasa da dama, ciki har da Lamine Yamal, Lionel Messi, da Cristiano Ronaldo.

Ya ce ya yarda da hazakar Yamal ta zura kwallaye, ya kuma nuna girmamawa ga Messi, amma a karshe ya zabi Ronaldo a gaban Messi — kafin daga bisani ya ambaci kansa a matsayin dan wasan da zai fi kowa zura kwallaye a gasar.

Erling Haaland (Norway)

Duk da cewa dan kasar Norway din bai taba buga gasar cin kofin duniya ba tukuna, Haaland ya tabbatar da kansa a matsayin daya daga cikin mafi kyawun ’yan wasan gaba a duniya yana da shekaru 25.

Dan wasan gaban na Norway, wanda ke da tsayin kafa 6 da inci 5, ya zura kwallaye sama da 160 ga kungiyar Manchester City tun lokacin da ya koma kulob din a shekarar 2022, inda ya kafa tarihi daban-daban a can.

Tare da lashe kyaututtukan takalmin zinare (Golden Boots) da dama, kofunan Premier League da na Champions League, Haaland zai nuna bajintarsa a babban mataki na kwallon kafa na duniya.

Rabon da Norway ta fito a gasar cin kofin duniya ta FIFA tun a shekarar 1998, inda ta kai zagayen kungiyoyi 16 — gasar da aka kammala kwanaki 19 kafin a haifi Haaland.

Yayin da kwanaki kalilan suka rage a fafata gasar cin kofin duniya ta 2026, Haaland ya bayyana kudurinsa dalla-dalla.

Yayin da yake magana da hukumar FIFA kwanan nan, Haaland ya ce: “Ban taba ganin Norway a gasar cin kofin duniya ba a rayuwata, don haka ina tsammanin lokaci ya yi da za mu kasance a ciki.”

Vinicius Junior (Brazil)

Wanda ake daukarsa a matsayin daya daga cikin ’yanwasa mafi kwarewa ta fuskar dabara a duniya, Vini Jr. ko Vinicius ne ke dauke da fatan wannan kasa ta Kudancin Amurka da ke da matukar muhimmanci kan kwallon kafa, kuma shi ne zai jagoranci ’yanwasan gaba na Brazil a gasar.

Gwarzon boye na Real Madrid ya zura kwallaye 16 tare da taimakawa aka zura guda 5 a kakar wasan da ta gabata. Ya kuma jagoranci kungiyar wajen lashe kofunan zakarun Turai na UEFA Champions League guda biyu.

Ganin cewa Brazil ba ta sake lashe kofin duniya ba tun shekarar 2002, kungiyar karkashin jagorancin Carlo Ancelotti za ta dogara ne ga dan wasan gefe Vinicius domin dawo da tagomashin tawagar.

Vinicius ya ce ba Brazil ce kasa daya tilo da ake ganin za ta yi nasara ba, yayin da ya nuna kwarin gwiwa mai karfi ga kansa, abokan wasansa, da kuma jagorancin Ancelotti domin cin kofin a karo na shida.

“Ni ne wanda kowa ke magana a kai yanzu saboda na yi kakar wasanni biyar ko shida masu kyau a Real Madrid kuma na shafe shekaru ina tsakanin mafi kyawun ’yanwasa a duniya,” in ji shi a wata hira da aka yi da shi kwanan nan.

“Wannan babban nauyi ne. Kuma wannan shi ne nauyin da nake so, saboda na san zan iya yin fiye da haka, in inganta, in ci gaba da bunkasa, kuma na san inda zan iya takawa saboda burina a koyaushe yana da girma sosai.”

Harry Kane (England)

Ana kallon Harry Kane a matsayin daya daga cikin kwararrun masu zura kwallo a raga na duniya. Duk da cewa ba shi da irin siffofin jiki na Haaland ko Mbappe, yana da kwarewa ta musamman wajen sanin inda zai tsaya da kuma samar da sarari.

Dan wasan mai shekaru 32 shi ne wanda ya fi kowa zura kwallaye a tarihin kasar Ingila da kwallaye 78 a wasanni sama da 110 da ya buga.

Shi ne na biyu a jerin wadanda suka fi kowa zura kwallaye a tarihin gasar Premier League da kwallaye 213. Tare da kungiyar Bayern Munich kuwa, ya zura kwallaye 98 a kakar wasanni 3 kacal a gasar Bundesliga.

Bayan nasarar da Ingila ta samu da ci 1-0 a wasan sada zumunta da kasar New Zealand a birnin Tampa, ya rage fargaba game da tsananin zafin da ake yi a Arewacin Amurka, inda ya bayyana cewa yana cikin koshin lafiya kuma yana dokin fara gasar.

“Mu kwararrun ’yanwasa ne. Dukkanmu mun yi kyakkyawan shiri domin tunkarar wannan gasa tare da taimakon ma’aikatanmu... saboda haka ina tunanin idan aka zo gasar, zafi ba zai zama matsala ba.”

Kane yana da muhimmanci sosai ga Ingila har ta kai tsohon dan wasan gaba Chris Sutton ya yi amfani da kalamai cewa idan har Kane “zai sanar da yin ritaya daga buga wa kasar wasa a wannan yammaci, kowa zai canza tunani nan take game da damar Ingila a gasar cin kofin duniya, kuma kwarin gwiwar tawagar zai kau.”

Ousmane Dembele (France)

Wani dan kasar Faransa na daban a cikin jerin sunayen, Ousmane Dembele, babban danwasa ne ga kungiyar Paris Saint-Germain kuma ya riga ya taimaka wa kungiyar tasa wajen lashe kofunan Champions League guda biyu a jere.

Wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or ta shekarar 2025 ya koma PSG ne a shekarar 2023 bayan wani lokaci mai wahala da ya fada a Barcelona.

Tare da gudu mai ban mamaki da kwarewar zura kwallaye, Dembele ya hadu da Mbappe da kuma danwasan Bayern Munich Michael Olise domin kafa ’yanwasan gaba guda uku mafi hatsari a gasar.

Dembele ya mayar da hankali sosai kan gasar, yayin da yake kallon irin kalubalen da ke gaba.

“Akwai tawagogi da yawa da ake kyautata zaton za su yi nasara, mun sani cewa [Argentina] ita ce mai rike da kofin duniya a halin yanzu, don haka babu shakka suna daya daga cikin wadanda ake gani za su yi nasara. Haka ma [Spain], wadda ta lashe kofin Turai a 2024. [Ingila], [Portugal], [Jamus]. Akwai kuma kungiyoyi masu wahala sosai kamar [Brazil], [Ecuador], Portugal. Tawaga ce mai wuya. Akwai wadanda aka fi amfani da su amma idan wasa ya fara, maza 11 ne da maza 11, babu sauran batun wanda aka fi sani. Dole ne in tsaya tsayin daka,” kamar yadda ya shaida wa ESPN.

Lionel Messi (Argentina)

Ana iya cewa ɗan wasa mafi tarihi mai kyau shi ne, Lionel Messi, wanda zai cika shekaru 39 a watan Yuni nan, kana shi zai jagoranci ƙungiyar Argentina a gasar.
Ko a wannan shekarun, Messi ya ci gaba da zama babban ɗan wasa wa ƙasarsa, inda ya lashe duk wata kyauta da wasan ke samarwa.

Dan wasan wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or sau takwas zai sake bayyana a gasar cin kofin duniya a karo na shida kuma zai jagoranci 'yan wasansa wajen riƙe kambun.

Messi ya dade yana shirye-shiryen tare da tawagar ƙungiyar kafin wasan farko na Argentina a ranar 16 ga Yuni inda zakarun za su fafata da Algeria a filin wasa na Arrowhead da ke Kansas City, Missouri.

An kwantar da shi a wasan sada zumunci da suka yi da Honduras a ranar 7 ga Yuni saboda ciwo da samu a cinyarsa tun daga ƙarshen watan Mayu, inda yake yin atisaye na musamman.

Kan damar da Argentina take da shi na sake maimaita matsayinta na zama zakara, a wata hira da aka yi da shi kwanan nan Messi ya shaida cewa, "Dole ne mu yi farin ciki, kamar yadda 'yan Argentina ke yi koyaushe, amma kuma dole ne mu san cewa akwai wasu waɗanda suka fi son wannan dama a gabanmu waɗanda suke cikin yanayi mai kyau ", kamar irinsu Faransa, Spaniya, Brazil da Portugal wadanda suke rike da matsayinsu masu ƙarfi.

 Cristiano Ronaldo (Portugal)

'Yan wasa kalilan ne suka cimma abin da Ronaldo yake da shi. Dan wasan gaban Portugal ya kware a fanninsa na taka leda, inda ya kai ga mataki mafi girma na kwarewa a wasan kwallon kafa.

Dan wasan mai shekaru 41 shine mafi ko wane dan wasa yawan cin kwallaye a tarihin kwallon kafa, da kwallaye fiye da 970. Shi ne babban mai zura kwallaye a kungiyoyin kasa da kuma a gasar zakarun Turai ta UEFA.

Sai dai, nasarar da ya taba samu tare da tawagar kasarsa ita ce a wasan Euro ta 2016.
Yayin da gasar cin kofin duniya ta kasance babbar gasa daya tilo da ta rage masa ya samu rayuwarsa, Ronaldo zai yi kokarin tabbatar da kambun a abin da ake sa ran zai zama wasansa na karshe a gasar.

Bayan nasarar da Portugal ta samu a kan Chile da ci 2-1 a ranar 6 ga Yuni, Ronaldo ya tabbatar wa magoya baya cewa kada gwiwoyinsu su yi sanyi da wasannin sharar fage, yana mai cewa: "Ba mu bayar da komai a wadannan wasannin ba saboda akwai babban aiki a gabanmu. Waɗannan wasannin galibi don sharar fage ne da kuma shiri. Don haka bai kamata mutane su yi hukunci kan kungiyar kwallon kafa ta Portugal bisa ga wasannin sada zumunci ba. Abin da ya fi muhimmanci shi ne abin da za mu nuna a lokacin da aka soma gasar cin kofin duniya ta FIFA."

 Jude Bellingham (Ingila)
La'akari da makomar 'yan wasan Three Lions, Bellingham ya haɗa halaye da yawa waɗanda suka sa shi zama ɗaya daga cikin mafi kyawun 'yan wasan tsakiya a duniya.

Yana iya zura kwallo daga wuri mai nisa,  kana yana da dabaru, da kuma ƙwarewar babbar wasa, sannan yana iya rike jagoranci da shekarunsa 22 kacal.

Yana iya cin kwallaye ta hanyar harba ƙwallon zuwa raga daga nesa da filin bugun fenariti.

Tuni Bellingham ya buga wasanni 46 tare da Ingila kuma zai kasance ɗaya daga cikin manyan sunayen a gasar.

Duk da matsayinsa na ɗaya daga cikin fitattun 'yan wasa a duniya, Thomas Tuchel, manajan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ingila, ya aika wa Bellingham saƙo a bayyane, yana mai gargaɗin ɗan wasan tsakiya na Real Madrid cewa matsayinsa a cikin 'yan wasan farko na Ingila ba shi da tabbas.

"Yana ɗaya daga cikin kananan ‘yanwasa, kuma ya san yana ɗaya daga cikin waɗanda za su fara wasa, amma muna da 'yan wasa 14 ko 15 da za su iya soma wasan. Za a iya canza matsayinsu a koyaushe, amma a yanzu ina ganin akwai 'yan wasa 14 ko 15 da suka dace kuma Jude yana ɗaya daga cikinsu," kamar yadda Tuchel ya shaida wa manema labarai a ranar Litinin.

 Mohamed Salah (Masar)
Ɗaya daga cikin kwararrun 'yan wasan Afirka, Mohamed Salah, ya samu damar sake kasancewa a cikin zakarun gasar cin kofin duniya a karo na biyu a shekarar 2026.
Ɗan wasan gefen mai shekaru 33 yana da tarihi da kyaututtuka da dama a sunansa, ciki har da kyaututtuka biyu na ɗan wasan Afirka na shekara da kyaututtuka uku na PFA Player of the Year.

Bayan fafatawa a wani kakar wasa da Liverpool, ya sanar da cewa zai bar ƙungiyar bayan shafe shekaru tara masu ban mamaki yana taka mata leda, Salah zai yi iya ƙoƙarinsa don jagorantar tawagar Pharaohs don samun tikitin gasar cin kofin duniya na farko wa Masar tare da sake tabbatar da cewa yana ɗaya daga cikin mafi kyawun dan’wasa.

Masar tana cikin rukunin G tare da Belgium, Iran, da New Zealand, inda za su buga wasan farko da Belgium a ranar 15 ga Yuni.
 Salah, wanda ke jagorantar ƙungiyar a gasar cin kofin duniya da zai buga na ƙarshe, ya jaddada burinsa, da gwazo da kuma gaskiyarsa game da ƙalubalen da ke gabansu.

A jawabinsa na baya-bayan nan, Salah ya mayar da hankali kan cika burinsa na ƙasa maimakon hasashen kwazonsa, yana mai bayyana hakan a matsayin wata dama ga Masar ta yi tasiri sosai tare da fatan wataƙila ta samu nasarar cin kofin duniya a karon farko.

"Manufarmu ita ce mu wakilci ƙwallon ƙafa ta Masar cikin alfahari tare da faranta wa al'ummar Masar rai ta hanyar yin wasanni masu gayatarwa da kuma sanya sunan Masar a babban wasan ƙwallon ƙafa na duniya," in ji Salah a ranar Litinin.

Arda Guler (Turkiyya)

"Hasashen kakar" gasar zakarun Turai ta UEFA ya mayar da hankali kan tawagar Turkiyya a gasar cin kofin duniya.
Arda Guler yana da ƙwarewa ta musamman kuma yana iya taka leda a wurare da matsayi daban-daban .

Turkiyya ta sake dawo wa gasae bayan shafe shekaru 24, inda Güler wanda a (yanzu yake da shekaru 21) yake a matsayin ɗaya daga cikin fitattun 'yan wasan ƙungiyar tare da wasu kamar Kenan Yıldız na Juventus.
Guler ya jaddada cewa Turkiye na da burin yin tasiri kuma ba za ta ji tsoron wani abokin hamayya a gasar ba.
"Muna matukar farin ciki game da wannan gasar cin kofin duniya. A karo na karshe da muka je gasar, ba’a haife ni ba. Mun samu labarin ne daga iyayenmu da 'yan'uwanmu. Mun yi kokari sosai don samun gurbin shiga gasar. Muna son mu nuna cewa ba mu zo nan don mu koma baya ba... Ba ma tsoron kowa!"

Turkiyya ta kasance mai ƙwazo kuma ba a doke ta ba a wasannin da suka gabata, ciki har da nasarar da ta samu a kan Venezuela da ci 2-1 a ranar 6 ga Yuni inda Güler taimaka wajen samun wannan nasarori.

Babban kocin Vincenzo Montella ya bayyana cewa Arda "yana da girmamawa a Turkiyya" a matakai "kamar irin na Maradona a Napoli,"  yana mai jinjinawa baiwar Güler, fahimtarsa, sanin wasa, da kuma kokarin yin wasa a ko wane yanayi na matsi.

Abokan wasan ƙungiyar sun kira shi "cikakken ɗan wasa" wanda zai iya zura kwallaye, taimakawa, da kuma tasiri a wasanni daga ko wane matak .
Turkiyya na fatan samu nasara a matakin rukuni ko ma kai wa mataki mai nisa bisa dogara kan Güler.

Achraf Hakimi (Morocco)

Achraf Hakimi na ɗaya daga cikin mafi kyawun ‘yan baya masu kai hari gaba a duniya, wataƙila mafi kyawu a Afirka a halin yanzu, kuma shi ne fuskar ƙungiyar ƙasarsa ta “Atlas Lions”.

Hakimi ya jagoranci Morocco zuwa wasan ƙarshe na AFCON da semi-final ɗin Kofin Duniya na 2022. Ƙalilan 'yan wasa ne ke da zafin naman shi.

Wannan babban ɗan bayan na PSG zai yi ƙoƙarin maimaita neman nasarar da tawagarsa ta samu a Qatar a 2022.

Keftin ɗin na Morocco, wanda yake buga hannun dama, wanda kuma ke sauya wasan zai buga kofin duniya a karo na uku (2018, 2022, 2026) kuma ya riƙa bayar da ƙwarin gwiwa ga tawagarsa, yana cewa burinsu shi ne yin nisa fiye da zagayen kusa da na ƙarshe a 2022: "Me zai hana mu yi mafi kyau fiye da a Qatar? Wannan burinmu ne!"

Ana ci gaba da magana kan Morocco a matsayin mai yiwuwa ta zama abin mamaki, kuma samun keftin mai zafin nama babban ƙwarin gwiwa ne ga magoya baya da tawagarsa.

Idan Atlas Lions za su sake ba duniya mamaki, Hakimi ba shakka zai kasance muhimmin ɗan wasa wajen jagorantar harin daga gefen dama.

Bruno Fernandes (Portugal)

Dan tsakiya na Manchester United ya kasance ɗaya daga cikin mafi kyawun ‘yan wasa a duniya tun lokacin da ya shiga Red Devils a 2020.

Tun lokacin da ya shiga United, ya bayar da taimako fiye da 70 kuma ya zura kwallaye fiye da 70.

Mai shekaru 31 yana da babbar damar zama muhimmin ɗan wasan Portugal a gasar, bisa ga yanayin sa a wannan kakar.

Duk da cewa Ronaldo yana nan a matsayin fuskar ƙasar da kuma keftin, masana da koci-koci suna ƙara kallon Fernandes a matsayin jagora a filin ƙwallon wanda ke tafiyar da tawagar.

A shekarunsa 31 kuma a mafi kyawun yanayinsa, mataimakin keftin ɗin na Portugal yana zama abin kwaikwayo kuma mai tsara wasa a kulob ɗin na Roberto Martinez.

Fernandes ya bayyana cewa yana son lashe Kofin Duniya "ba don Portugal kadai ba, amma don duka gudunmawar da Cristiano ya ba wasan ƙwallon kafa." Abokan wasa da magoya baya suna ganinsa a matsayin wanda ke taka rawa a manyan lokuta, yayin da masana ke cewa damar Portugal ta lashe gasar za ta ƙaru sosai idan Martínez ya gina tawagar a kan Fernandes kuma ya ba shi kullum kwallo — kamar yadda aka yi amfani da shi a Manchester United a ƙarƙashin wasu manajoji.

Michael Olise (Faransa)

Wani ɗan wasan Faransa na cikin jerin wanda ya kamata a kalla. Ɗan wasan gefe na Bayern Munich ɗin ya zura kwallaye 15 kuma ya kasance mai muhimmanci ga nasarar tawagarsa.

A kaka biyu ta farko da ya yi tare da babban kulob din Jamus, ya zura kwallaye 41 kuma ya bayar da taimako sau 46.

Ko da yake ya buga wasa sau 15 kacal da Les Bleus, Olise ya cika abin da da yawa ke kira ɗaya daga cikin layukan gaba mafi haɗari a duniya tare da Mbappe da Dembele.

Manajan Bayern Munich Vincent Kompany ya yi imanin Olise "tabbas zai kasance ɗaya daga cikin mafi kyawun 'yan wasa a duniya", yayin da kocin Faransa Didier Deschamps ya lura cewa Olise yana kawo "sauki sosai" kuma shi "mai kawo bambanci ne". A gefe guda, abokin wasa Harry Kane ya bayyana shi a matsayin "mafi kyawun dan gefen dama a duniya."

Raphinha (Brazil)

Kamar Vinicius Junior, Raphael Dias Belloli – wanda aka fi sani da Raphinha – zai kasance mai muhimmanci ga Brazil wannan bazara. Bayan komawa Barcelona daga Leeds United a 2022, dan shekara 29 wanda ke buga Kofin Duniya na biyu, ya taka rawa wajen nasarar Barca.

Yayin da Vinicius ke jan hankali a tawagar Brazil, ba za a iya manta Raphinha ba kuma zai kasance mai muhimmanci ga tawagar a Kofin Duniya.

Koci Carlo Ancelotti na Brazil ya bayyana shi a fili a matsayin "mafi kyawun ɗan wasa a duniya wajen kai hari sosai", wanda ya sa ake saka shi a farkon wasa kuma abin kwaikwayo ga sauran ‘yan wasa.

Ancelotti ya aika Raphinha a matsayin dan tsakiya mai kai hari, inda yake haɗa wasa, yanka da zura ƙwallaye da kuma samar da dama.

Ga tsohon tauraron Brazil Ronaldinho Gaucho, wannan ba wasan Neymar Junior ne kawai ba ne.

"Brazil yanzu tana da wani ɗan wasa mai iya yanke hukunci a wasanni kuma da kuma taka rawa a cikin matsin lamba. Idan Raphinha ya kawo salon Barcelona dinsa zuwa Kofin Duniya, zai iya zama ɗaya daga cikin manyan 'yan wasan gasar," in ji Ronaldinho a cikin sabon bayaninsa.