Ministan Sufuri da Ababen More Rayuwa na Turkiyya, Abdulkadir Uraloglu ya bayyana cewa Turkiyya da Saudiyya sun cim ma wani gagarumin mataki a dangantakarsu ta sufuri da harkokin dabarun jigilar kayayyaki bayan sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna a fannonin sufuri da layin dogo.
A wata sanarwa da ya wallafa a dandalin sada zumunta na NSosyal a ranar Talata, Uraloglu ya ce yarjejeniyar za ta buɗe sabon babi na haɗin gwiwa da musayar ƙwarewa da fasaha a fannoni daban-daban, tun daga cibiyoyin dabarun jigilar kayayyaki zuwa sabbin hanyoyin gudanar da ayyukan sufuri.
Ya ce ƙasashen biyu suna kuma ƙarfafa haɗin gwiwarsu a bangaren layin dogo ta hanyar gina tsarin haɗin kai mai ɗorewa, musamman a fannoni kamar fasaha, ababen more rayuwa, horas da ma’aikata da bunƙasa albarkatun ɗan’adam.
“Muna fatan waɗannan matakai da za su taimaka wajen inganta haɗin kai, kasuwanci da ci gaban yankinmu za su amfani ƙasashenmu biyu na dogon lokaci,” in ji shi.
Ma’aikatar Sufuri da Ababen More Rayuwa ta Turkiyya ta bayyana cewa Uraloglu da Ministan Sufuri na Saudiyya, Saleh bin Nasser Al-Jasser, ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar.
Wata madadin hanyar kasuwanci ta duniya
Uraloglu ya ce: “Tun kafin shekarar 2012, yawan jigilar kayayyaki tsakanin ƙasashenmu biyu a duk shekara ya kai 20,000.
“Ko da yake a yanzu wannan adadi ya ragu sakamakon sauye-sauyen da suka faru a yankin, burinmu shi ne mu ɗaga haɗin gwiwarmu har ta zarce wannan mataki.”
Ya ƙara da cewa ƙasashen biyu na bibiyar ci gaban da ake samu a hanyoyin sufuri ta Syria, Jordan da Iraki, yana mai cewa:
“Gwaje-gwajen jigilar kayayyaki guda biyu da aka gudanar daga Turkiyya ta cikin Iraki zuwa Saudiyya sun nuna a sarari cewa wannan hanya na da amfani kuma za ta iya aiki yadda ake bukata.”
Yarjejeniyar “Fahimtar Juna kan Haɗin Gwiwa a Fannin Ayyukan Dabarun Jigilar Kayayyaki” na da nufin sauƙaƙa gina cibiyoyin dabarun jigilar kayayyaki, gudanar da ayyukansu, musayar ƙwarewa da kuma aiwatar da ayyukan haɗin gwiwa.
A gefe guda kuma, “Yarjejeniyar Fahimtar Juna kan Haɗin Gwiwa a Fannin Layin Dogo” tana da manufar ƙarfafa haɗin gwiwa da aiwatar da shirye-shirye na bai ɗaya a dukkan bangarorin harkar layin dogo.
A farkon wannan wata, Abdulkadir Uraloglu ya bayyana cewa Turkiyya na shirin sabunta tsohon layin dogo na Hejaz tare da tsawaita shi zuwa ƙasar Oman domin samar da wata sabuwar hanyar kasuwanci ta duniya da za ta kasance madadin mashigin ruwa na Strait of Hormuz.
Ya ce Turkiyya na son farfaɗo da wannan tsohon layin dogo domin amfani da shi wajen yawon buɗe ido da kuma harkokin sufuri na zamani.
A cewarsa, matakin farko shi ne haɗa Turkiyya da birnin Aleppo ta hanyar amfani da layin da ke haɗa Aleppo da Damascus da Jordan, yayin da ake ci gaba da tattaunawa da mahukuntan Saudiyya kan ci gaban aikin.
















