Kungiyar Houthi ta Yemen ta fada a ranar Litinin cewa za ta sanya dokar "dakatar da zirga-zirgar jiragen ruwa na Isra'ila gaba daya" a Bahar Rum, tana mai gargadin cewa za a sake kai hari kan jiragen ruwa da ke da alaƙa da Isra'ila saboda tashin hankalin yankin da ke dada karu.
'Kungiyar ta yi barazanar haramta wa Isra'ila jigilar kayayyaki ta Tekun Bahar Rum gaba daya yayin da rikicin yankin ke karuwa’
Kungiyar ta kuma ce ta kai hare-haren makamai masu linzami kan abin da ta bayyana a matsayin wuraren da Isra'ila ke kai hari a yankin Jaffa, tana mai ikirarin cewa hare-haren sun cimma manufofinsu da "yanda yakamata."
Hare-haren da ka iya faɗaɗa rikicin yankin
A cikin sanarwar da ta fitar, kungiyar ta ce an kai hare-haren makamai masu linzami ne a matsayin martani ga hare-haren Isra'ila a Iran, Falasdinu, Lebanon, Iraki, da kuma Yemen, tana mai kari da cewa za ta zafafa kai hare-haren sojinta daidai da abubuwan da ke faruwa a ƙasa.
"Mun tabbatar da cewa za mu mayar da martani mai zafi ga zafafan hare-hare,’’ in ji ƙungiyar, tana mai ƙari da cewa ayyukanta za su dada yawa.
Zuwa yanzu dai Isra'ila ba ta mayar da martani nan take kan sabbin iƙirarin ba. Sai dai da safiyar yau Litinin, an rufe sararin samaniyar Isra'ila na ɗan wani lokaci bayan an kawar da wani makami mai linzami da aka harba daga Yemen, a cewar rahotannin kafofin watsa labarai na Isra'ila.
Hakan dai, ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da faɗaɗa tashe-tashen hankula a yankin, ciki har da sanya shingen makamai masu linzami na Iran a arewacin Isra'ila bayan harin da ta kai a yankunan kudancin Beirut.
Kazalika Isra'ila ta kai hare-hare a yammaci da kuma tsakiyar Iran, inda aka ruwaito fashewar abubuwa a birane da dama, ciki har da Tehran, Isfahan, da Tabriz.


















