Nijeriya ta bayyana a ranar Jumma’a cewa tana shirin mayar da ‘yan ƙasar fiye da 1,000 gida daga ƙasar Afirka ta Kudu yayin da tashin hankali mai alaƙa da ƙin jinin baƙi ke ƙaruwa a ƙasar, wadda ta daɗe da zama wurin zuwan baƙi ‘yan Afirka da aka yi wa rijista da waɗanda ba a yi wa rijista ba.
Yunƙurin da Abuja ke yi na zuwa ne bayan Ghana ta mayar da ɗaruruwan ‘yanƙasarta gida daga Afirka Ta Kudu a matsayin wani martani ga jerin zanga-zanga da tashe-tashen hankali da ke mayar da hankali kan baƙi.
A ranar Alhamis ne aka fara tantance ‘yan Nijeriya masu neman komawa gida bisa raɗin kansu, kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, Kimiebi Ebienfa ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP ranar Jumma’a.
"Cikakken adadin bai fito ba tukunna," kamar yadda ya bayyana. "Muna dakon fiye da mutum 1,000."
A wata sanarwar da aka buga ranar Talata, ofishin jakadancin Nijeriya a Pretoria ya ce ya cim ma "yarjejeniyar ɗaga ƙafa da hukumomin masu masauƙin baƙi" domin waɗanda ke da "laifuka masu alaƙa da shige da fice" za a ba su damar tafiya a jirage su koma gida maimakon a tsare su.
Afirka ta Kudu, wadda kafin kwanan nan ita ce ƙasar da ta fi ƙarfin masana’antu a nahiyar, ta daɗe tana jan hankalin ma’aikata daga faɗin yankin.
Amma tun da ƙasar tana fama da rashin aikin yi da ya shafi kashi 30 cikin 100 na mutanen cikinta, tana fuskantar ɓarkewar zanga-zangar ƙin jinin baƙi -- ciki har da sabunta tashin hankali a cikin ‘yan makonnin nan.
Tashe-tashen hankali na baya bayan nan sun tayar da muhawara mai zafi a faɗin Afirka dangane da ƙin jin baƙi da ci-rani da giɓin da ke tsakanin kalaman kishin Afirka da haƙiƙanin abin da ke fuskantar tafiye-tafiyen ci-rani a nahiyar.
Wani wa’adin da wata ƙungiyar ‘yanƙasa mai gwagwarmayar korar waɗanda suka shiga ƙasar ba bisa ƙa’ida ba nan da ranar 30 ga watan Yuni ya ƙara fargabar samun tashin hankali, bayan da ɓarkewar tashin hanklai a baya ya haddasa rasa rayukan gomman mutane.
A watan da ya gabata, Ghana ta mayar da wasu mutane 300 a wani ɓangare na farko na mayar da mutanen da hukumomi suka ce za su kai jumullar ‘yan Ghana 800.
Gwamnatin Afirka ta Kudu ta ce tana ƙara matsa ƙaimi a kan hana kwararar baƙin haure, amma ta yi kira ga ‘yan ƙasar kada su ɗauki doka a hannunsu.
Akwai kimanin baƙi miliyan uku da ke zama a Afirka ta Kudu, ko kuma kashi 5.1 cikin 100 na adadin jama’ar ƙasar, in ji hukumar ƙididdiga ta ƙasar.
Fiye da kashi 63 cikin 100 daga cikinsu sun fito ne daga ƙasashe 16 da ke mambobin ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙsashen kudancin Afirka.










![Masar ta yi kira ga kwamitin tsaro na MƊD ta dakatar da faɗaɗa [harin] da Isra'ila ke yi a Lebanon](https://d2udx5iz3h7s4h.cloudfront.net/2026/4/25/67480fcc1bc16e3971fbb70d/image/35fa6aac64e41c9240c09651b2ba0fb1be4eb5b1e1ca009d1c3d191c8f65622b.webp?width=512&format=webp&quality=80)
