Yadda bankunan Nijeriya da kwastomominsu suka yi asarar naira biliyan 134 a zambar intanet
NIJERIYA
3 minti karatu
Yadda bankunan Nijeriya da kwastomominsu suka yi asarar naira biliyan 134 a zambar intanetRahoton ya nuna cewa an yi yunƙurin aikata zambar intanet har ta kimanin naira biliyan 187.79 cikin shekaru shida, yayin da aka tafka asarar da aka tabbata ta kai naira biliyan 134.48.
An gargadi masu mu'amalar kudi ta intanet su kiyaye matakan kariya daga zamba. / Reuters

Babban Bankin Nijeriya, CBN, ya bayyana cewa bankunan ƙasar da kwastomominsu sun yi asarar jimillar kuɗi har naira biliyan 134.48, sakamakon zamba ta intanet a tsakanin shekarar 2020 zuwa 2025.

Wannan ya faru ne daidai lokacin da ƙasar ke ci gaba da rungumar hanyoyin biyan kuɗi na zamani, da shigar da mutane harkar hada-hadar kuɗi ta banki, da kuma fasahar sadarwa ta kudi.

Bayani kan yawan asarar kuɗin na ƙunshe ne a rahoton “Nigeria Payments System Vision 2028”, wanda CBN ya wallafa a shafinsa na intanet.

Rahoton ya nuna cewa an yi yunƙurin aikata zambar intanet har ta kimanin naira biliyan 187.79 cikin wa’adin shekaru shida, yayin da aka tafka asarar da aka tabbata ta kai naira biliyan 134.48.

Asarar ta shafi hanyoyin biyan kuɗi da dama, ciki har da ta cire kuɗi ta cikin banki, da ta injunan ATM, da takardun cek, da kasuwancin yanar gizo, da hada-hadar banki ta intanet, da bankin wayar hannu, da injunan POS, da sauran hanyoyin biyan kuɗi na zamani.

Masana harkokin tsaron intanet, wato cybersecurity sun buƙaci hukumomi da bankuna su ƙarfafa tsaron intanet, da kuma wayar da kan jama’a kan zambar intanet da yadda za su kaucewa faɗawa tarkon miyagu. 

Don kare kai daga mazambatan intanet, ga wasu matakai da ya kamata mutane su ɗauka:

Ɓoye bayanan banki

Kada ka taɓa bayyana lambobin sirrinka na banki ga kowa, wato lambar PIN, da lambar CVV da ke bayan katin ATM, da lambobin tantancewa da ake turo maka ta waya wato (OTP).

Masana na gargaɗin cewa kada mutum ya bayyana waɗannan lambobi ga kowa, har da ma waɗanda suke iƙirarin cewa su ma’aikatan banki ne.

Ƙarfafa tsaro a intanet

A riƙa amfani da hanyoyi da dabaru masu matuƙar tsaro a intanet, kamar amfani da kalmomin sirri masu tsawo, kuma a cakuɗa su da lambobi da haruffa da alamomi na musamman.

Sannan a riƙa sauya kalmomin sirri daga lokaci zuwa lokaci. Kazalika a riƙa amfani tsarin tsaro mai matakai biyu ko mai matakai da yawa, wato two-factor authentication, ko multi-factor authentication, duk inda hakan zai yiwu.

Lura da mu’amalolin intanet

Bankuna da masu ba da sabis na biyan kuɗi suna da tsarin sa-ido kan zamba. Don haka, yana da kyau ka tuntuɓi bankinka nan-take idan ka ga wani abu da ba ka saba da shi ba a asusunka.

Wayar da kai

Masana suna bayar da shawarar cewa yana da matuƙar muhimmanci jama’a su riƙa neman sani game da wasu muhimman abubuwa da suka shafi intanet da hada-hadar kudi a zamanance.

Hakan zai sa su iya kaucewa faɗawa tarkon miyagu ta sanin ƙarin sabbin hanyoyi da dabarun kariya da ake ƙirkirowa ko sabuntawa.