Lalata takardar kudi ta naira babu ƙaƙƙautawa da kuma sarrafa naira ta hanyar da ba ta dace ba na jawo matsalolin tattalin arziki a Nijeriya, kamar yadda gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso ya yi gargaɗi ranar Talata.
Ya yi wannan maganar ne a wajen ƙaddamar da ƙungiyar jakadu na musamman don kare martabar naira a babban birnin ƙasar, kamar yadda kafar Channels ta ruwaito.
Cardoso ya ce kuɗin da bankin ke kashewa wajen samar da takardun kuɗin tsaftattu masu ɗorewa zai iya samun tasirin da ake so ne kawai idan mutanen ƙasa suka yi amfani da kuɗin yadda ya kamata bayan an fara aiki da ita.
Ya jaddada cewa kare takardar kudin ƙasar dole a kalle shi a matsayin nauyin da ya rataya a kan kowa.
Ya ce, “A lokacin da aka lalata takardun kuɗi ko kuma aka sarrafa su yadda bai dace ba, za su lalace cikin sauri fiye da yadda ake tsammani. Wannan na ƙara tsadar kuɗin maye gurbinsu da ingancin yawon kuɗi da kuma ƙaƙaba nauyin asarar da za a iya kaucewa a kan ƙasa.
“Saboda haka kare takardar kudinmu ba damuwar aiki ba ne kawai ga Babban Bankin Nijeriya; lamari ne na nauyin da ya rataya a kan ‘yan ƙasa.”
Gwamnan na CBN ya bayyana cewa naira takarda ko leda ba ce kawai, yana mai cewa tana aiki ne a matsayin abar musaya da doka ta yarda da ita da taimakawa wajen harkokin kasuwanci da tallafa wa ajiyar kuɗi da zuba jari, kuma kawo yanzu alama ce bayyananniya ta haƙiƙanin Nijeriya da ‘yancin kanta.
Ya ce duk wata takardar kuɗi tana ba da labari game da ƙasar ta hanyar hotunan fitattun ‘yan Nijeriya da alamomin ƙasa da alamomin tsaro da aka saka a ciki domin tabbatar da ƙwarin gwiwar ‘yan ƙasa a tsarin kuɗin.
Cardoso, wanda ya ƙaddamar da kulob ɗin jakadun mai ɗalibai 175 da aka zaƙulo daga makarantu bakwai a matsayin mambobinsa na farko, ya ce an tsara shirin ne domin samar da al’ada ta girmamawa ga takardar kuɗi ta ƙasa tsakanin matasa ‘yan Nijeriya da kuma amfani da tasirinsu wajen samar da sauyin halayya a faɗin gundumomin ƙasar.
Ya ce sauyin halayya mai ɗorewa ya fi samuwa ne ta hanyar ilmantarwa, yana mai cewa matasa su ne suka fi janyo sauyi a tsakanin iyali da makarantu da ma al’umma bakiɗaya.










