Mataimakin Shugaban Amurka JD Vance ya tafi Switzerland yayin da manyan masu shiga tsakani daga Iran suka isa Zurich gabanin zuzzurfar tattaunawa mai muhimmanci don aiwatar da yarjejeniyar farko da nufin kawo ƙarshen yaƙin Gabas ta Tsakiya.
Vance ya tabbatar da cewa zai mayar da hankali kai-tsaye wajen tabbatar da ci-gaba mai ma’ana a shirin nukiliyar Iran da kuma batun tsagaita wuta a Lebanon, wanda yake da rauni.
"Waɗannan su ne manyan abubuwa biyu da nake ganin ya kamata mu mai da hankali kansu," kamar yadda Vance ya fada wa 'yan arida kafin ya tashi daga sansanin jirage sama na Joint Base Andrews, inda ya nuna cewa zai iya shiga tattaunawar ne kawai ta tsawon "kwana ɗaya ko biyu".
An shirya tattaunawa a Switzerland a ranar Juma'a, amma an ɗage yayin da Isra'ila ta kai munanan hare-hare a a Lebanon.
Bayan ƙarin tashe-tashen hankula, duka Isra'ila da Hezbollah sun zargi juna da keta sabuwar yarjejeniyar tsagaita wutar, wadda take cikin yarjejeniyar wucin gadi da Amurka da Iran suka sanya wa hannu.
Vance ya bayyana halin da ake ciki a Lebanon a matsayin "abin da yake ainihin ingantuwa," yana mai ƙarawa da cewa: "Wannan abu ne da za mu ci gaba da kula da shi domin tabbatar da cewa... Isra'ila da Lebanon duka suna zaune lafiya kuma cikin aminci. Babbar matsala ita ce wani zai harba sannan wani zai mayar da martani, kuma irin matsalar 'ƙwai da kaza' ce inda dole a dakatar da harbe-harben na ɗan lokaci har sai tsagaitawar wutar ta tsaya da ƙafarta."
Manyan masu shiga tsakani na Amurka Jared Kushner da Steve Witkoff sun riga sun kasance a Switzerland suna kula da zuzzurfar rtattaunawa ta ƙwararru.
A gefe guda, tawagar tattaunawar Iran ta isa Zurich a daren Asabar.
A cewar gidan talabijin na jihar Iran IRIB, tattaunawar za su gudana a fadar Bürgenstock a ƙarƙashin tsarin Yarjejeniyar Fahimtar Juna ta Islamabad ,kamar yadda Ma'aikatar Harkokin Waje ta Pakistan ta tabbatar.











