Kisan wata mata da wasu matasa suka yi kuma suka kona gawarta a Jihar Kaduna ya haifar da kakkausar suka da martani kan yadda jama’a suke daukar doka a hannunsu bayan an zargi mutum da aikata wani babban laifi.
Wannan mummunan lamari mai ban tausayi ya faru ne bayan yaduwar jita-jitar cewa matar, mai suna Ummulkhairi, tana sace yara a Marabar Jos, a Jihar Kaduna a karshen makon jiya.
Rahotanni na ce lamarin, wanda ya haddasa fargaba a yankin, ya faru ne sakamakon damuwar da mazauna yankin ke da ita game da zargin yawaitar sace-sacen yara a garin.
Rahotonni sun bayyana cewa marigayar wacce malamar Islamiyya ce tana kan hanyarta ne ta zuwa wani taron wa’azi lokacin da wasu matasa suka zarge ta da yunkurin sace wasu yara.
Daga baya aka kaita wani ofishin ’yansanda da ke kusa domin ba ta kariya da kuma gudanar da bincike.
Sai dai lamarin ya rincabe a daidai lokacin da daruruwan matasa suka far wa ofishin ’yansandan suna neman da a danka ta a hannunsu.
Ko da yake akwai wasu daga cikin dangin matar da suke zargin ’yansanda ne suka mika ta ga matasan kafin kisan ta. Amma ’yansandan ba su fito kai-tsaye sun tabbaar ko musanta hakan ba a cikin wata sanarwa da suka fitar ranar Lahadi.
Sanarwar wacce jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yansanda a Jihar Kaduna DSP Mansir Hassan ya fitar, ta ce rundunar ta yi Allah wadai da kisan matar. Sannan sanarwar ta ci gaba da cewa an ajiye ta a ofishin ’yansanda da yake yankin ne saboda tsaron lafiyarta da kuma gudanar da bincike.
Duk da wannan kokarin na ’yansanda, a cewar sanarwar, wasu gungun mutane sun afka tare da kewaye ofishin, inda suka ci karfin jami’an da ke bakin aiki, suka kuma kwace matar, sannan suka kashe ta tare da ƙona gawarta a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Zaria.
Rundunar ’yansanda ta bayyana wannan aika-aikar a matsayin dabbanci, babban laifi wanda ya saba wa doka.
DSP Mansir Hassan ya ƙara da cewa, an kama mutane da dama waɗanda ake zargi da hannu a lamarin, kuma ana ci gaba da farautar sauran masu hannu a ciki. Ya ce, an fara cikakken bincike, kuma duk waɗanda suka aikata wannan laifi za su fuskanci hukunci.
Ita ma Kungiyar Kare Hakkin dan Adam ta Amnesty International ta yi Allah wadai da babbar murya kan mummunan kisan gillan da aka yi wa marigayiyar, kamar yadda kungiyar ta bayyana a shafinta na Facebook ranar Litinin.
Sannan ta bukaci rundunar ’yansandan kasar ta gudanar da cikakken bincike kan zargin cewa wasu jami’anta ne suka mika matar ga gungun matasan da suka kashe ta.
Amnesty International ta ce matsalar ɗaukar doka a hannu tana ɗaya daga cikin manyan barazanar da ke fuskantar ’yancin rayuwa a Nijeriya.
Su ma masana harkokin shari’a da lauyoyi da sauran jami’an tsaro suna yawan kiraye-kiraye da jan hankalin da jama’a kan illolin da ke tattare da yadda mutane suke daukar doka a hannunsu.
Su kuwa ‘yan kasar da dama da lamarin ya fusata suke yi kan hukumomin Nijeriya su bi wa wannan mata kadi, su dauki tsattsauran mataki kan duk wanda aka tabbatar yana da hannu, ta yadda za a yi wa iyalanta adalci, sannan hakan ya zama darasi ga masu sha’awar daukar doka a hannu nan gaba,














