| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Shugaban Nijar Abdourahamane Tiani ya fara ziyarar aiki a Turkiyya
A ranar Laraba ne shugaban na Nijar ya taso daga ƙasar ta yammacin Afirka domin fara ziyarar aiki bisa gayyatar da takwaransa na Turkiyya ya yi masa, kuma Tiani ya sauka a Ankara a daren Alhamis.
Shugaban Nijar Abdourahamane Tiani ya fara ziyarar aiki a Turkiyya
Shugaba Abdourahamane Tiani ya gana da Ministan Harkokin Waje Hakan Fidan, da Ministan Tsaro Yaşar Güler da Ministan Makamashi Alparslan Bayraktar. / AA

Shugaban Jamhuriyar Nijar Janar Abdourahamane Tiani ya isa Turkiyya a ranar Laraba da daddare domin fara ziyarar aiki.

Wata sanarwa da gwamnatin Turkiyya ta fitar ta ce shugaban na Nijar da ke yammacin Afirka zai kai ziyarar ne bisa gayyatar takwaransa na Turkiyya.

“Bisa gayyatar Shugaba Recep Tayyip Erdoğan, Shugaban Jamhuriyar Nijar Abdourahamane Tchiani zai kawo ziyarar aiki Turkiyya ranar 4 ga watan Yuni na shekarar 2026,” kamar yadda daraktan watsa labaran gwamnatin Turkiyya Burhanettin Duran ya bayyana a wani saƙon da ya wallafa shafin X .

“Yayin tattaunawar, za a sake duba duk ɓangarori na dangataka tsakanin Turkiyya da Nijar, kuma za a yi nazari kan matakai na sake haɓaka haɗin kai,” in ji sanarwar.

Ziyara mai muhimmanci

Ya ƙara da cewa: “Shugabannin biyu za su yi musayar ra’ayi game da abubuwan da ke faruwa a yankin da kuma duniya.”

A wata sanarwa da Fadar Gwamnatin Nijar ta fitar ranar Laraba ta ce Shugaba Tiani ya kama hanyar Turkiyya, “inda zai kai ziyarar aiki da ƙawance, da nufin ƙarafa haɗaka tsakanin ƙasashen biyu.

Sanarwar ta kuma zayyano manyan jami’an gwamnatin Nijar masu yawa suka take wa Tiani baya a yayin ziayarar, waɗanda ta ce duka suna da muhimmanci a fannonin ci-gaban kasa.

Ta ce ganin irin mininstocin da ke cikin tawagar ya nuna cewa hukumomin Nijar a shirye suke su jaddada haɗaka da Turkiyya a ɓangarori da dama, waɗanda suke da muhimmanci wajen bunƙasa tattlin arziki da masana’antu da tsaron Nijar.

Manyan jami’an gwamnatin Nijar da suke cikin tawagar sun haɗa da Ministan Tsaron Ƙasar Salifou Mody da Ministan Lafiya Garba Hakimi da Ministan Ababen More Rayuwa Salissou Mahaman da Ministan Haƙar ma’aidinai Ousmane Abarchi.

Har wa yau tawagarsa ta ƙunshi Ministan Harkokin Waje Bakary Yaou Sangaré da Shugaban Ma’aikatan Shugaban ƙasa kuma Mai Magana da Yawun Gwamnati Soumana Boubacar da MinistanTattalin Arziki da Kuɗi Maman Laouali Abdou Rafa da Ministan Noma Mahaman Elhadj Ousmane da Ministan Makamashi Amadou Haoua da Ministan Ciniki da Msana’antu Abdoulaye Seydou da Jakadan Nijar a Turkiyya Salou Adama Gazibo