| Hausa
DUNIYA
4 minti karatu
Amurka da Iran sun kammala tattaunawa a matakin ƙoli a Switzerland, a cewar masu shiga tsakani
Ministan Harkokin Wajen Iran ya jinjina wa sabon ci-gaba da aka samu a tattaunawar Switzerlan, yana nuni da sabbin matakan tsagaita wuta a Lebanon, yayin da masu shiga tsakani, Pakistan da Qatar ke ƙoƙarin ganin al'amura sun daidaita a yankin.
Amurka da Iran sun kammala tattaunawa a matakin ƙoli a Switzerland, a cewar masu shiga tsakani
Iran da Amurka sun samu 'ci gaba mai ban kwarin gwiwa' a tattaunawa mai muhimmanci, in ji masu shiga tsakani. / Reuters

An kammala zagaye na farko na tattaunawa tsakanin manyan jami'an Amurka da Iran a Switzerland, in ji masu shiga tsakani, bayan fara tattaunawar cikin damuwa sakamakon sanarwar da Iran ta yi na sake rufe Mashigar Hormuz, sannan Shugaban Amurka Donald Trump ya maimaita barazanar dawo da kai hare-hare Iran.

Wata sanarwa ta haɗin gwiwa daga ƙasashen da ke shiga tsakani, Qatar da Pakistan ta ce Amurka da Iran sun amince da taswirar da za a bi zuwa yarjejeniya ta ƙarshe cikin kwanaki 60. Za a ci gaba da tattaunawa mai zurfi har zuwa ƙarshen mako, a wurin shaƙatawa mai tsaunuka na Burgenstock mallakin Qatar a Switzerland, in ji sanarwar da Ma'aikatar Harkokin Wajen Qatar ta fitar.

Sanarwar ta ce ɓangarorin sun amince da wata hanya ta kawo ƙarshen rikici a Lebanon kuma sun buɗe hanyoyin sadarwa don taimakawa wajen tabbatar da wucewar jiragen kasuwanci ta mashigar da ake takaddama a kanta cikin aminci.

A cikin wani rubutu a kafar sada zumunta, Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi ya ce ƙasarsa ta samu rangwamen izini kan fitar da mai da kayan da suka danganci albarkatun mai, da sakin wasu kadarorin da aka hana taɓawa, da ƙaddamar da shirin sake ginawa da ci-gaban Iran.

Fadar White House ba ta yi wani martani nan da nan ba lokacin da aka tambaye ta ko tattaunawar ta ƙare kawo yanzu.

Kamfanin dillancin labarai na Tasnim mai alaƙa da gwamnatin Iran, ya ce, fara tattaunawa kan batutuwan nukiliya na buƙatar fara aiki da sauran sassan yarjejeniyar fahimtar juna, ciki har da sakin kadarorin da aka hana taɓawa da rangwamen Amurka da ke ba da izinin fitar da mai daga Iran.

A wani ɓangaren kuma, Araghchi ya faɗa a safiyar Litinin cewa tattaunawar da aka yi da Amurka a Switzerland, wadda Pakistan da Qatar suka shirya, ta kawo cigaba mai ma'ana wajen kawo ƙarshen yakin Lebanon da rage matsin tattalin arzikin Iran.

"Tsayawa da dagewar shiga tsakani da Pakistan da Qatar suka yi sun kawo babban ci-gaba wajen kawo ƙarshen Yakin Lebanon. An soke takunkumi akan fitar da mai da kayan albakartun man fetur, an kawar da toshewar da aka yi wa tashohin jiragen ruwa, an saki wasu kadarorin da aka hana taɓawa, kuma an ƙaddamar da babban shirin sake ginawa da ci gaban Iran," in ji Araghchi a dandalin sada zumunta na Amurka, X.

"Gwaji na farko na ainihi: sashen kawar da rikicin Lebanon," in ji Araghchi.

"Abubuwa masu ‘yar sarƙaƙiya"

A cikin wata sanarwa daban, ministan harkokin wajen Iran ya bayyana matakan na diflomasiyya a matsayin wani ɓangare na babban mataki da ƙasar ke ɗauka.

"Daga filin ƙwallon kafa zuwa teburin tattaunawa zuwa fagen yaki, duk wani mataki da muka ɗauka a matsayin Iraniyawa, wani ɓangare ne na babbar gwagwarmaya: kare martaba da ɗaukakar mutanenmu masu daraja," in ji shi.

Yarjejeniyar ta buƙaci sake buɗe Mashigar Hormuz, wadda ke da muhimmanci wajen jigilar makamashi ta duniya, da kawo ƙarshen dukkan hare-hare, ciki har da a Lebanon, inda Isra'ila ke ci gaba da kaddamar da miyagun hare-hare.

A yayin tattaunawar a Switzerland, inda jami'an Amurka da Iran suka haɗu a gaban masu shiga tsakani na Qatar, Vance ya nuna rahin tasirin tashin hankali a Lebanon, yana cewa an samu ci gaba wajen kawo ƙarshen ayyukan soji a can.

"Wannan abubuwa koyaushe suna da ‘yar sarkakiya," in ji shi.

Can a Amurka, Trump ya yi barazanar dawo da kai hare-hare a Iran idan ba ta tsawatar wa abokan ƙawancenta ba.

"Dole ne nan-take Iran ta dakatar da masu yi mata yaƙi waɗanda take biyansu da kyau a Lebanon daga haifar da matsala," Trump ya rubuta a kafar sada zumunta, a bayyane yana nufin Hezbollah. "Idan ba su yi ba, za mu sake afka wa Iran da ƙarfi sosai, kamar yadda muka yi makon da ya gabata, sai ma ya fi wancan ƙarfi!!!"

Ko da yake Trump yana yi wa Iran barazana, Vance ya shaida wa 'yan jarida cewa shugaban Amurka ya "nemi mu buɗe sabon shafi wajen sauya dangantakarmu da mutanen Iran."

Duk da sanarwar sabuwar tsagaita wuta a Lebanon a ranar Juma'a, ba a ga alamun kawo ƙarshen rikici a ƙasar ba.

Iran ta faɗa a ranar Asabar cewa, sakamakon haka, ta sake rufe mashigar, wacce rufewa na kusan watanni hudu ta haifar da babbar matsala ga jigilar makamashi ta duniya a tarihin wannan zamani.

Kafar yaɗa labarai ta Fars ta Iran ta ambaci wata majiyar soja tana faɗa a ranar Lahadi cewa ba a ba da sabbin izini ga jiragen ruwa su ketare ba har sai an ba da sanarwa ta gaba.

Ranar Lahadi ta zama wata rana mafi shiru a Lebanon a cikin wasu ‘yan kwanaki, inda har zuwa cikin dare ba a bayar da rahotannin wani babban tashin hankali ba, bayan kwanaki biyu Isra'ila tana kai munanan hare-hare.

Rumbun Labarai
Netanyahu ya fusata Trump bayan ya caccaki shirin Amurka na sayar wa Turkiyya F-35: Rahoto
Ana fargabar mutuwar 'yan ƙabilar Rohingya fiye da 500 bayan kifewar jiragen ruwa a gaɓar Myanmar
Masu ceton dabbobi na taimaka wa tsuntsaye tsira daga bazara mai zafi
Ƙirkirarriyar Basira, ƙarfin intent da ƙa’idojin aikin jarida
Yawan masu kamuwa da cutar kansa na iya kusan ninkuwa nan da shekarar 2050
Mai tsaron bayan Argentina ya ce alƙalan wasan Gasar Kofin Duniya 'na aiki mai kyau'
An kona gini mai kama da masallaci a Arewacin Ireland  a yayin da ‘yansanda ke gudanar da bincike
An samu rahotannin cin zarafin mata kusan 9,800 a shekarar 2025, fiye da ninki biyu kan na 2024: MDD
Mene ne takunkuman CAATSA kuma ta yaya cire su da Amurka za ta yi zai amfani Turkiyya?
Shugaban Koriya ta Arewa ya je kallon gwajin makami mai linzami mai iya ɗaukar nukiliya
Tafiyar al'ajabin Cape Verde ta ƙare, amma ƙasar Afirkan ta fice daga gasar kofin duniya da suna
TikTok da Youtube sun rufe shafukan yara miliyan 4.7 a Indonesia bayan matakan gwamnati
NATO za ta bayyana biliyoyin daloli a wasu sabbin kwangilolin tsaro a taron Ankara
An ɗaure 'yan Nijeriya sha biyu a Jamus saboda 'zamba ta hanyar soyayya'
Venezuela ta ayyana dokar ta-ɓaci bayan tagwayen girgizar ƙasa, ana fargabar dubbai sun mutu
Tagwayen girgizar ƙasa masu ƙarfi sun afka wa Venezuela, an ba da rahoton ɓarna da yawa
Amurka ta sa takunkumi kan wani ɗan canji dan Nijeriya da wasu kamfanoni kan zargin tallafa wa Daesh
Majalisar Dattijan Amurka ta umarci Trump ya kawo ƙarshen yaƙin Iran
Starmer ya yi murabus daga matsayin Firaministan Birtaniya
Ɗanwasan film ɗin Breaking Bad Giancarlo Esposito ya karɓi Musulunci a Saudiyya: rahoto