Sakatare Janar na ƙungiyar ƙawancen tsaro ta NATO Mark Rutte ya ce ƙawancen nasu zai sanar da gomman biliyoyin daloli kan sabbin kwangiloli na tsaro a taron wata mai zuwa a babban birnin Turkiyya, Ankara, yayin da ƙasashe mambobin ƙawancen ke neman faɗaɗa da kuma ƙarfafa samar da kayayyakin soji da kuma ƙarfafa ikon tsaro gaba ɗaya.
Da yake magana a wani taron cibiyar nazari ta hulɗar ƙasa da ƙasa ta Atlantic Council Front Page a Washington ranar Alhamis, Rutte ya ce dole ƙawayen da ke cikin NATO su ƙara ƙoƙari su mayar da ƙarfin tattalin arzikinsu zuwa ƙarfin soji yayin da ƙalubalen tsaro ke ƙaruwa a duniya.
Babban jami’in na NATO ya ce taron na Ankara ya “ma fi muhimmanci ” kan taron shekarar da ta gabata a birnin Hague, yana mai jaddada muhimmancin aiwatar da alƙawurran ƙawancen.
"Muna buƙatar tabbatar da cewa muna sauya ƙarfin tattalin arzikinmu zuwa ƙarfin soji," kamar yadda Rutte ya bayyana.
"Wannan na nufin shawo kan rarrabuwar masana’antun tsaro na ƙasashe a ɗaya ɓangare na tekun Atalantika da kawar da ɓata lokaci a nan Washington da kuma ci-gaba da ajiye hanyar ƙirƙire-ƙirƙire a faɗin ƙawancen."
Faɗaɗa haɗin kai
Rutte ya ce taron NATO da za a yi tsakanin ranar 7 zuwa 8 ta watan Yuli a Ankara zai ba da damar nuna ci-gaba wajen faɗaɗa haɗin kai na masana’antu da kuma ƙara ƙwarewa na haɗa abubuwa.
"Za mu yi shelar gomman biliyoyi daloli na sabbin kwagiloli," in ji shi, yana mai ƙarawa da cewa kamfanonin ƙera kayayyakin tsaro a faɗin ƙawancen suna ƙara yawan ababen da suke samarwa domin iya biyan buƙatar da ke ƙaruwa.
Rutte ya kuma tabbatar da goyon bayan NATO ga Ukraine, yana mai cewa shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy zai halarci taron.
"Shugaba Zelenskyy zai kasance tare da mu a Ankara," in ji shi.
"Muna tsammanin mu nuna masa da dukkan ‘yan Ukraine cewa goyon bayanmu mai ɗorewa ne kuma [mu] tuna wa Shugaban Rasha Vladimir Putin cewa ba za mu je ko ina ba."












