| Hausa
DUNIYA
5 minti karatu
Tafiyar al'ajabin Cape Verde ta ƙare, amma ƙasar Afirkan ta fice daga gasar kofin duniya da suna
Tafiyar al'ajabin Cape Verde ta ƙare cikin baƙin ciki bayan ta galabaitar da Argentina a wasan da ta sha kaye da 3-2. Duk da cewa 'yan Afirkan sun sha kaye, amma sun kafa sunansu a cikin manyan duniya.
Tafiyar al'ajabin Cape Verde ta ƙare, amma ƙasar Afirkan ta fice daga gasar kofin duniya da suna
Tawagar Cape Verde ta bai wa mutane da yawa mamakin yadda ta riƙe Argentina har zuwa ƙarin lokaci bayan sun tashi canjaras a minti 90 na farko / Reuters

Abin da Vozinha ke so kawai a wannan gasar cin kofin duniyar shi ne mahaifiyarsa ta ganshi yana wasa.

Ya samu wannan — da ma abin da ya fi hakan .

Cape Verde ba ta yi nasara a wasa ɗaya ba a wannan gasar cin kofin duniyar, amma da alama wannan ba wata matsala ba ce.

Karon farko da tawagar ta Afirka ta bayyana wannan fagen abu ne da ba za a iya mantawa da shi ba , saboda golanta mai shekara 40 wanda ya kusa kafa wani labarin ƙwallon ƙafa da za a ƙirga a matsayin ɗaya daga cikin bazatan da suka fi ƙarfi a tarihi wasanni.

Tafiyar al’ajabin Cape Verde ya ƙare ranar Juma’a a zagaye na ƙasashe 32, inda tawagar Blue Sharks ta faɗi a hannun Lionel Messi da kuma ƙasar da ke kare kanbun kofin duniya Argentina — kamar yadda aka tsammani.

Yadda aka tashi wasa: Zakaru 3, gwarzayen bazata 2, a cikin ƙarin lokaci— kamar yadda a iya cewa mutane kaɗan ne suka tsammanci hakan.

Kuma a hakan ne tafiyar ta ƙare.

Sun fara ne da tashi canjaras da Sifaniya a wasansu na farko a gasar, inda Vozinha ya jagorance su , lamarin da ya janyo ƙoƙarin da aka yi na duniya domin kai mahaifiyarsa Amurka domin ta kalli wasannin matakin rukunin .

An ƙara samun ƙarin wasu wasanni biyu da aka tashi canjaras da suka taimaka wa Cape Verde ficewa daga matakin rukuni zuwa matakin sili ɗaya ƙwale.

"Abin da muka cim ma , mun so mu nuna abin da zai yiwu ga ƙananan ƙasashe . Da babbar zuciya , da za ka iya imani kuma ka yi mafarkin cewa komani na iya faruwa ," kamar yadda mai tsaron baya da aka haifa a Ireland Pico Lopes ya shaida wa manema labarai.

"Ina fatan cewa wannan tawagar ta ƙarfafa gwiwar wasu matasan Cape Verde su kasance a nan nan gaba . Mun nuna cewa abu ne mai yiwuwa. Mun nuna abin da za ka iya yi idan ka isa wannan matakin kuma ka haɗu da wasu daga cikin tawagogi da suka fi ƙarewa a duniya."

"Gasar cin kofin duniya babbar aba ce a gare mu, domin aba ce da muka daɗe muna so . Mun samu shiga gasar kuma muka cim ma burinmu , ba wai gare ni ni kaɗai ba ko kuma tawagar ƙasar kaɗai ba, face ga dukkan al’ummar Cape Verde gabaɗaya," a cewar Vozinha, wanda a halinyanzu ba shi da kulob.

"Muna alfahari da dukkan abubuwan da muka cim ma . A bayyane yake cewa ba mu ji daɗi ba da sakamakon saboda mun so mu kai zagaye na gaba.

"Mun san cewa muna fuskantar abokan gaba masu ƙarfi — zakarun duniya— amma ina son na gode wa ɗaukacin hukumar ƙwlalon ƙafa [ta ƙasa] da kuma ɗaukacin tawagar ," in ji shi .

Daka ƙarshe, sai da Messi ya zura ƙwallo ɗaya da kuma taimakawa wajen zura ƙwallo ɗaya da bugun tazara cikin ƙarin lokaci, sa’o’i biyu da rabi da fara wasa, kafin Argentina mai ƙarfi ta tsira daga Cape Verde.

‘Babu wanda zai tambayar cewa mene ne Cape Verde’

An tura Argentina maƙura sosai inda Vozinha ya tsaya tsayin daka a kan tawagar da ake ganin ta fi ƙarfi a duniya– da kuma ɗanwasan da ya fi iya murza leda a duniya – a sau da yawa.

Vozinha ya tare aƙalla ƙwallaye masu muni huɗu da Messi ya buga a minti 60 na ƙarshe na wasan .

— Tare wani ƙwallo kai tsaye minti 63 da fara wasa bayan Messi ya yi ƙoƙarin buga ƙwallon da ƙarfi da ƙafarsa ta dama domin ƙwallon ya wuce golan zuwa cikin raga, inda golan ya taso daga kan layinsa domin tare ƙwallon da jikinsa.

— Wani bugun tazara daga Messi minti 73 da fara wasa wanda ke kan hanyarsa ta juyowa cikin raga ta dama ; hannun da Vozinha ya tura ya samu ya buge ƙwallon lamarin da ya tsayar da wasan kunnen doki 1-1 .

— Messi ya yi ƙasa-ƙsa a wani bugun tazara a cikin ƙarin lokaci ; Vozinha ya samu ya ga ƙwallon daga cikin ganuwar ‘yanwasan kuma ya sauƙa kan gwiwarsa inda ya samu ya tare ƙwallon .

— Daga ƙarshe cikin minti 15 na ƙarin lokaci, Messi ya samu wani ƙwallon da aka ture a cikin murabba’in fenareti kuma ya buga ta da ƙarfi. Vozinha ya kwanta ta hagu , inda ya ture wannan ƙwallon gefe.

Cape Verde, ƙasa mafi ƙaranci a fili da ta shiga gasar cin kofin duniya kuma wata ƙasa mai addadin mutanen da bai wuce kashi 1 cikin 100 na mutanen Argentina, za ta samu kuɗi dala miliyan $11 daga hukumar FIFA domin kaiwa wannan matakin a wannan gasar.

Amma , tawagr Blue Sharks ta sami abin da ya fi kudi . An ƙara saninsu a fage mafi girma a na ƙwallon ƙafa.

"A lokacin da muka samu shiga gasar cin kofin duniya , mun so mu je mu nuna cewa ya kamata a ce muna nan . Ina ganin a salon wasanninmu a matakin rukuni da wannan dare, mun nuna cewa za mu iya takara da wasu daga cikin tawagogi mafi ƙarfi a duniya," a cewar Lopes .

"Ɗaya daga cikin abubuwa masu faranta wa mutum rai da suka fito daga wannan gasar cin kofin duniyar shi ne babu wanda yanzu sai ya yi tambayar cewa mene ne Cape Verde .

"Sun san inda muke a kan taswirar duniya . Sun san yadda muke a matsayar tawaga. Ina ganin dukkan ‘yan Cape Verde a faɗin duniya waɗan suka sami ƙwarin gwiwar zama ‘yan wasan ƙwallon ƙafa, mun nuna musu hanya a yau."