Wata kotun Jamus ta ɗaure 'yan Nijeriya 12 saboda hannu a abin da aka kira "zamba ta hanyar soyayya" da almundahanar kuɗaɗe.
Kotun a birnin Munich ta faɗa a ranar Alhamis cewa, waɗanda aka samu da laifin suna tsakanin shekaru 34 zuwa 55, kuma an yanke musu hukuncin daurin shekaru daga 3 da watanni 4 zuwa shekaru 8 da rabi.
An same su da laifin kasancewa cikin wata cibiyar ƙasa-da-ƙasa da ake amfani da ita wajen gudanar da zamba ta hanyar soyayya sannan suna safarar kuɗaɗen da aka samu ta haramtacciyar hanya.
Kotun ta ce waɗanda aka yanke wa hukunci su kan yi amfani da sunaye na bogi, misali suna bayyana kansu a matsayin sojan Amurka da aka tura Gabas ta Tsakiya, domin tunkarar waɗanda za a yaudara a kafafen sada zumunta ko manhajojin haɗuwa, su yaudare su har su yarda suna cikin wata alaƙa ta kusa ko ta soyayya.
kashe kuɗin bogi
Daga nan sai a buƙaci waɗanda aka yaudara su aika kuɗi don taimakawa wajen biyan kuɗaɗen magani, ko kuɗaɗen tafiya ko na kwastam.
Kotun ta ce 'mata, ko tsofaffi, ko mutane masu nakasa' sun fi yawa a cikin waɗanda aka cuta.
Daga nan aka tura kuɗaɗen zuwa wata ƙungiya mai suna 'Neo Black Movement of Africa', wadda ake kira 'Black Axe', wadda ke Najeriya amma tana ayyuka a faɗin duniya.
A watan Afrilun 2024, 'yansandan Jamus sun gudanar da jerin kamen mutane, suna neman 'yan wannan ƙungiya, bayan shekaru ana bincike da sa ido daga hukumomin leƙen asiri na cikin gida.
A lokacin aikin, 'yansandan Bavariya sun ce ba a bayar da rahotanni da dama ba, saboda waɗanda aka yaudara suna jin kunya da har suka bari aka yi musu haka.










